Home / Ilimi / A Gaggauce: Gwamnatin Jihar Katsina Ta Amince Da Biyan Miliyan 300 Ga Hukumar NECO

A Gaggauce: Gwamnatin Jihar Katsina Ta Amince Da Biyan Miliyan 300 Ga Hukumar NECO

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Katsina na cewa Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari ta amince da biyan kudi naira miliyan dari  300  ga hukumar shirya jarabawa da NECO domin a saki sakamakon jarabawar yara ta shekarun 2019 da 2020 da suka gabata.

Kwamishinan Ilimin Jihar Farfesa Badamasi Lawal Charanchi ya tabbatar da hakan a lokacin wata tattaunawa da ya yi da wata kafar yada labarai.

Kamar dai yadda aka bayyana cewa hukumar shirya jarabawa ta NECO ta rike sakamakon jarabawar wadansu jihohi cikinsu har da Jihar Katsina na shekarar 2019 da 2020.

Kamar dai yadda Kwamishina ilimi na Jihar Katsina Farfesa Badamasi Lawal Charanchi ya tabbatar cewa yawan kudin sun kai naira miliyan dari uku da Hamsin da hudu 354,518,215.25 dai dai.

 

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.