Home / Ilimi / Wani Wa’azi Daga Allah Da Tauhidi

Wani Wa’azi Daga Allah Da Tauhidi

Mustapha Imrana Abdullahi
Wata rana wani Direban mota da ke aiki a Kwalejin ilimin kimiyya da fasaha ta Gwamnatin tarayya da ke Kaduna, ya dauko wata Fara da ta makale a sandar share gilashin mota ( waifa) har yazo Kaduna tun daga garin Abuja ya na zuwa otal din motel da ke titin Waff da ake kira Muhammadu Buhari way ya na ajiye motar sai kawai wannan Farar da ya dauko daga Abuja ta tashi ta fada bakin wani Kadangare nan take ya cinye abin sa.
Direban tare da wadansu mutane sai suka kama mamaki su na cewa kyauta daga Allah tun daga garin Abuja an kawo masa Fara ya cinye hakika kyauta ce daga Allah.
Sai kuma wani mai neman arzikin da ya nemi a rokar masa Allah ya samu kudi haka kuwa aka yi, bayan an roka masa sai Allah madaukakin Sarki cikin ikonsa ya na fita wata kofa da zaton samun arzikinsa sai Kura ta Cinye shi baki daya, a kissar cewa shi zai samu gidan Aljannah ita kuma Kura ta na jin yunwa ne Allah ya ciyar da ita, shi kuma ya samu babban rabo a kiyama da gidan Aljannah.
Sai kuma wata kyautar daga Allah da wani Bawan Allah da ya tsinci Kudi naira dubu Ashirin a gidan Wanka da bahaya.
Bayan ya shiga wani gidan Wanka nan take ya tsinci dubu Ashirin.
Bayan ya fita waje sai ga mai kudin sun hadu da shi a waje ya na ta neman kudinsa, ba da bata lokaci ba ya ce hakika na tsinci kudi dubu Ashirin amma kullum na yi Sallah sai na roki Allah ya ba ni kudi dubu Ashirin kuma ita ce Allah ya ba ni don haka ba wata magana.
Bayan an fara hayaniya sai ga wani mutum da ya ji ana cece- kuce ya ce me ya faru aka gaya masa yadda abin yake sai ya dauko dubu Ashirin din ya ba ainihin mai kudin ya ce wancan Allah ne ya bashi.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.