Home / Labarai / A JIHAR SAKKWATO ZA A DADE ANA TUNA AIYUKAN SANATA AMINU WAZIRI TAMBUWAL

A JIHAR SAKKWATO ZA A DADE ANA TUNA AIYUKAN SANATA AMINU WAZIRI TAMBUWAL

….Tambuwal ya yi Ayyukan Alkairi A Jihar Sakkwato

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon irin kishi da son ganin ci gaban Jihar Sakkwato tare da al’ummar Jihar yasa Tsohon Gwamna kuma Zababben Sanata a yanzu Barista Aminu Waziri Tambuwal ya aiwatar da dimbin ayyukan da za a dade ana amfanarsu a Jihar.

Kamar yadda Honarabul Atiku Muhammad Yabo Sarkin Yakin Yabo, ya shaidawa wakilinmu cewa ayyukan da Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya aikawar a lokacin ya na Gwamnan Jihar Sakkwato abin a yaba ne tare da yin alfahari a kansu a koda yaushe.

Domin mutanen Jihar Sakkwato za su dade suna tunawa da irin ayyukan da Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya aiwatar kasancewar aiki ne da kowa ke gani a fili jama’a na amfana da su.

A kwai inda aka baro baya ana samun wadansu wuraren da suke zamar wa mutane wani alakakai sakamakon irin halin da suke ciki amma a wurare da dama matsaloli sun zama sai tarihi kawai kasancewar sun ga mu da kokari irin na Aminu Waziri Tambuwal.

Ga dai irin wasu ayyukan da ya aiwatar dalla – dalla kamar haka

1 Aikin gina Gadar sama a Dandima a cikin birnin Sakkwato

2 Aikin gina Diflomat a Rijiyar Doruwa

3 Aikin Tagwayen hanyar Maituta

4  Aikin gina asibitin koyarwa na jami’ar Mai alfarma Sarkin Musilmi Sa’ad Abubakar

5 Aikin ginin Rijiyoyin burtsatse huda dubu 1,500 a fadin kananan hukumomi 23 da suke Jihar Sakkwato, domin samar da ruwa lita miliyan daya da rabi.

6 Aikin ginin asibitin Firimiya a kowace mazabar dan majalisar Dattawa a Jihar Sakkwato, da kuma asibiti mai cin gadaje dari 700

7 Aminu Waziri ya gyara gidajen Hakimai sama da 83 a kananan hukumomi 23 na Jihar.

8 Daukar Malaman makaranta sama da dubu 3000 da ke aiki a kananan hukumomi 23 na Jihar

9 Aikin samar da na’urar transfoma sama da dari 200 domin samar da ingantacciyar wutar lantarki a kananan hukumomi 23 da ke fadin Jihar

10 Amincewa da kuma sayen Injuna sana da dari 300 domin gyaran Ruwan sha a dukkan kananan hukumomi 23 na Jihar Sakkwato

11Aikin samar da Dakin karatu na zamani mai amfani da Yanar Gizo a jami’ar Abdullahi Fodiyo da ke Sakkwato

12 Aikin gyare – gyaren asibitin kwararru na Jihar Sakkwato

13 Aikin ginawa da gyaran titunan Shagari

14 Aikin samar da wadataccen Ruwa a mabera tare da kawo saukin Bankin duniya.

Honarabul Atiku Muhammad Yabo Sarkin Yakin Yabo ya ce dukkan wadannan ayyukan na nan ana iya ganinsu domin dimbin jama’a miliyoyi na yin amfani da su wanda hakan ba karamar nasara ba ce ga Jihar Sakkwato da kasa baki daya a matsayin tarayyar Najeriya.

Inda ya ci gaba da bayanin cewa an aiwatar da aiki kamar haka

15 Aikin ginin da ya lashe makudan biliyoyin naira a makarantar sakandare a karamar hukumar Bungudu

16 Aikin ginin katafaren ginin da ya lashe makudan miliyoyi a makarantar Sakandare ta Abdullahi Bara’u a Dogon Daji a karamar hukumar Tambiwal

17 Aikin gina Sabuwar Sakatariyar karamar hukumar Shagari

18 Aikin gyara  na bai daya ko- ina da Ina a babbar kotun Jihar Sakkwato

19 Aikin gina wa da gyaran babbar kasuwar Jihar Sakkwato

20 Aikin gyaran sabon Sogis da hukumar tara kudin haraji na Jihar Sakkwato.

21 Aikin ginin titin da ke bayan gari a Kware a karamar hukumar kware.

22 Aikin ginin baidaya da gyare – gyare a dukkan makarantun Sakandare na kimiyya da Fasaha a dukkan fadin kananan hukumomi 23 da ke Jihar Sakkwato

Kamar yadda mu zanta da shi Honarabul Atiku Muhammad Yabo nan gaba za a ci gaba da kawo maku ayyukan da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Sanata a yanzu Aminu Waziri Tambuwal ya aiwatar a tsawon shekaru Takwas da ya yi yana jagorantar Jihar.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.