Home / Labarai / CIKAR ALKALI BELLO MUHAMMAD SHINKAFI SHEKARU 20 YA NA ALKALANCI

CIKAR ALKALI BELLO MUHAMMAD SHINKAFI SHEKARU 20 YA NA ALKALANCI

….Shekaru 20 Masu Albarka tare da gaskiya da tsare Amana

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Dauda Lawal Dare ya bayyana murna tare da farin cikinsa bisa irin yadda Mai shari’a Bello Muhammad Shinkafi, ya cika shekaru Ashirin ya na Alkalanci bisa gaskiya da adalci a Jihar Zamfara.

Alhaji Ahmad Garba Yandi wakilin Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Dauda Lawal Dare, a wurin babban taron da aka shirya a garin Gusau domin taya murnar cika shekaru 20, ya ce Gwamna na farin ciki da murna game da wannan taron na bikin cika shekaru 20 Gwamnatin jiha da iyalansa duk na murna da farin ciki da wannan bawan Allah.

Alkalin babbar kotun Jihar Zamfara Alkali Bello Muhammad Shinkafi, ya bayyana cikakkiyar gamsuwarsa da irin Ni’imar da Alllah ya yi masa na yin gadon Alkalanci kamar yadda Kakansa da Mahaifinsa baki daya suka yi Alkalanci.

“Ni na fito ne daga tsatson Alkalai domin kakana daMahaifina duk sun yi Alkalanci don haka a yau na zama Alkali burina ya cika ko a yau na koma wa Allah burina ya cika”.

Alkali Bello Muhammad Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar jawabin godiya a wajen babban taron da aka shirya domin bikin cikarsa shekaru 20 ya na Alkalanci da yan uwa da abokan arziki tare da abokan da aka yi aiki da tare da su suka halarta a garin Gusa hedikwatar Jhar Zamfara a arewacin tarayyar Najeriya.

“Ni daman niyyata shi ne in zama Alkali kuma Alhamdulillah Allah ya biya Mani bukata ta, ko yau Allah ya dauki raina bukata ta ta biya”.

“Alhamdulillah, Alhamdulillah, hakika duk wanda yazo yaga irin mutane  da suka taru a nan sai godiya ga Allah madaukakin Sarki kawai domin irin muhimman mutanen da suka taru a nan hakika abin yi wa Allah godiya ne kwarai, ina yi wa duk wanda yazo nan godiya kwarai nagode nagode”.

Da yake nasa jawabin Alkalin Alkalai na Jihar Zamfara Alkali Dahiru Muhammad cewa ya yi mai shari’a namu ne mutumin mu ne mun yi aiki tare da dadewa, mun yi aiki karkashinsa tun ya na C R mu kuma muna kananan Alkalai tun a lokacin yake girmama mu ya Karrama mu wallahi muna godiya kwarai.

“Don haka ni ina tabbatarwa jama’a cewa mutumin kirki ne mai son jama’a da rikon gaskiya, Allah kara masa lafiya da zama lafiya ya sa mu sanye lafiya mu da shi

A nasa jawabin Khadi Kabir Hafiz Gusau cewa ya yi hakika muna ta ya Alkali Bello Muhammad murna kasancewar ya na da kyakkyawan tarihi a gidan shari’a domin ya iya shari’a ba cin hanci ga gaskiya ga kuma sauran abubuwan da ake bukata ga Alkalai.

“Muna rokon Allah ya kara tsare shi ya shiryar da shi da mu baki daya ya kuma yi mana arzikin gama aikin lafiya dukkan alkairan da yake nema a cikin aikin Allah ya Sada shi da su, abubuwan da ake tsoro Allah ya kare shi ya tsare shi ya kare shi Allah ya kare mu baki daya don albarkar Alkur’ani.

Tsohon Babban Sakatare ma’aikatar Gona a Jihar Zamfara Alhaji Altine da ya bayar da dan Takaitaccen tarihin rayuwarsu tun suna dalibai yan makaranta.

“Masani ne a fannonin Lissafi da Turanci kwarai da gaske domin mutum ne tsananin kwakwalwa da ke lashe dukkan darussan da ake Koyar da mu muna dalibai”

Ko a wancan lokacin da muke matsayin dalibai a shi ke karbar kyautar dalibi mai hazaka a makarantar Usman Dan fodiyo Sakkwato

” na san ya karanta littafin Nobel har guda 1200 domin ya kara inganta turancinsa da kara kaifin basira”.

Ya ce Mai shari’a Bello Muhamamd Mutum ne idan ya yi ma alkawari zai yi kokarin cika alkawarin a koda yaushe ga shi kuma mutum ne mai son zumunci kwarai ga kowa da kowa.

A hagu zuwa Dama Alkali Bello Muhammad Shinkafi tare da Alkalin Alkalan Jihar Zamfara a wajen taron

Taron dai ya samu halartar maza da mata a ciki da wajen Jihar Zamafara domin taya Mai shari’a Bello Muhammad murnar cika shekaru sama 20 ya na alakalanci

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.