Home / Labarai / A Katsina Yan Sanda Sun Kama Jami’in Shigi Da Fici, Mutane Da Shanu 164

A Katsina Yan Sanda Sun Kama Jami’in Shigi Da Fici, Mutane Da Shanu 164

Imrana Abdullahi

Jami’an tsaron yan Sanda a Jihar Katsina a ranar Alhamis sun tsare wani mutum da ya ce shi Insifekta ne  da ke aiki a hukumar kula da shigi da ficin jama’a ta kasa tare da wadansu mutane biyar da aka samesu da Shanu 164  da ake zargin na sata ne

Abubakar Shafi’u, wanda ya ce shi jami’in hukumar kula shigi da ficin jama’a ne wanda aka bake kolinsu tare da sauran wadanda ake zargi ya shaidawa manema labarai cewa M9hammes Isah, Ibrahim Mohammed, Idris Mohammed, Usman Mohammed, Sa’idu Lawal dukkansu yan uwane da suke zaune a karamar hukumar Zurmi da ke Jihar Zamfara.


Shafi’u wanda ya ce shi jami’in hukumar kula da shigi da ficin jama’a ne ta Nijeriya da ke aiki a ofishinsu a Abuja, amma yanzu yana yin hutu ne shi yasa yake yi masu rakiya domin fitar da su daga Jihar Zamfara, wanda aka hanyar hakan aka tsare su.

Ya musanta cewa Shanun na sata ne amma an dauke su ne zuwa garin Potiskum da Buni Yadi  a Jihar Yobe, kuma masu Shanun ne suke dauke da shi saboda matsalar yan bindiga a Jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Katsina Gambo Isa ya tabbatar da cewa an samu nasarar kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis da misalin karfe 1: 30 na dare a kan iyakar Jibiya da garin Katsina sakamakon samun ingantaccen bayanin sirri da hadin Gwiwar jami’an yan sanda da kwastan suka samu cewa akwai wadansu mutanen da ke tare da manyan motoci uku makare da shanu bisa Rakiyar wani mai suna Shafi’u.

” Ana ci gaba da yin bincike a kan lamarin kuma muna sane da irin yadda ake samun matsalar satar Dabbobi, an kuma san yadda Jihohin Katsina da Zamfara suke da kuma tarihin Zurmi game da batun maboyar masu aikata laifi.

” zamu yi sako sako da irin wannan lamari ba, zamu ci gaba da gudanar da bincike har sai mun samo tushen wadannan Dabbobi kuma duk wanda aka samu da laifi za a gabatar da shi a gaban kuliya”.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.