Home / News / ADAM MUHAMMAD NAMADI ZAI FAFATA DA DUK WANI DAN TAKARA – UMAR

ADAM MUHAMMAD NAMADI ZAI FAFATA DA DUK WANI DAN TAKARA – UMAR

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
An bayyana dan takarar neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya karkashin PDP daga mazabar Kaduna ta tsakiya a Jihar Kaduna Adam Muhammad Namadi da cewa mutum ne da yake a shirye domin fafatawa da kowa ne dan takara.
Malam Umar wanda ya wakilci dan takara Adam Muhammad Namadi wajen karbar takardar satifiket na shaidar cewa an tantance shi a matsayin dan takarar neman kujerar majalisar wakilai karkashin jam’iyyar PDP daga mazabar Kaduna ta tsakiya.
Malam Umar ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan gabatar da wakilcin karbar takardar satifiket din bayan tantance Adam Muhammad Namadi a matsayin dan takara wanda kwamitin da uwar jam’iyya ta kasa ta aiko Kaduna domin aiwatar da aikin.
“Ai tun da dai an ba matasa damar yin takara hakika dan takara Umar Muhammad Namadi a shirye take domin fafatawa da kowa a wannan tsarin”. Inji Umar.
Jam’iyyar PDP ta kasa ce ta aiko da wani kakkarfan kwamiti da suka zo Kaduna domin tantance yan takarar neman kujerar majalisar wakilai ta kasa da majalisar Dattawa daga Jihar Kaduna karkashin PDP.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.