Home / News / NA FITO TAKARA DOMIN JAMA’A NE – SARDAUNA

NA FITO TAKARA DOMIN JAMA’A NE – SARDAUNA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
HONARABUL Usman Ibrahim  ( Sardaunan Badarawa) ya bayyana cewa ya fito takara ne domin taimakawa rayuwar dimbin al’umma ta inganta.
Honarabul Usman Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan an kammala tantance shi a matsayinsa na dan takarar kujerar dan majalisar Dattawa domin wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP.
Usman Ibrahim ya bayyana cewa ya fito ne ba domin kansa ba sai saboda kokarin inganta rayuwar jama’a ba domin kansa ba, idan don kaina ne ba zan fito ba”, inji Sardaunan Badarawa.
Ya ci gaba da cewa kamar dai yadda nake cewa ne ” ba ni da mai gida ba wanda ya Sanya ni, ni na Sanya kaina na aiki kaina kuma ina yi ne domin jama’a kuma ina ta yin addu’ar cewa wannan abu idan Allah zai ba ni ba domin jama’a ba ne kada ya ba ni, in kuma Allah zai ba ni don jama’a ne to, Allah ya ba ni musamman na wannan shiyyar ta mu Allah ya ba ni”.
Kuma ina fatan “Allah ya sa ni ne zan kawo karshen wannan matsalar ta tsaro da ke addabar al’umma”.
“Wasu mutane na cewa wai mun shigo PDP ne to, a wannan wurin tantance yan takara waye ya zo da rigar PDP a duk cikin jerin yan takarar nan baki daya? Ina son a gaya Mani shin akwai wani daga cikin masu neman wannan takara ta kujerar Sanata akwai wanda ya Sanya rigar PDP irin wannan da na sa a jikina, saboda haka ni ne asalin dan jam’iyyar PDP kuma dan takara domin yi wa jama’a abin da ya dace saboda haka rana kawai ake jira a rantsar da ni a matsayin Sanatan Kaduna ta tsakiya”. Inji Sardaunan Badarawa.
Usman Ibrahim ya kuma yi kira ga wadanda yake yin takara da su cewa idan Allah ya bashi sa’a su taho a tafi tare domin a samu cimma nasarar da kowa ke bukata”.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.