Uwar Gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana goyon bayanta ga masu zanga-zangar neman a ceci rayuwar jama’a ta fuskar tsaro.
Aisha Buhari ta buɗe wani sabon gangami a shafinta na Tuwita inda tayi kira ga #AchechiJamaa tuni dai mutane suka soma yaba mata akan yadda ta fito fili ta goyi bayan ƴan zanga-zangar.