Home / News / Gwamnan Jihar Zamfara Ya Dauki Aniyar Canza Wa Arewa Suna

Gwamnan Jihar Zamfara Ya Dauki Aniyar Canza Wa Arewa Suna

Gwamnan Jihar Zamfara Ya Dauki Aniyar Canza Wa Arewa Suna

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Dokta Muhammadu Bello Matawallen Maradun ya yi kira ga daukacin sauran Jihohin arewacin Nijeriya da su dauki aniyar canza tunanin da wasu ke yi cewa wai yankin Cima zaune ne.
Gwamnan ya dai yi wannan kiran ne lokacin da yake jawabi a kan irin yadda yake sayen zinari yana tarawa domin amfanin Jihar.
Gwamna Matawallen Maradun ya ci gaba da cewa Jiharsa ta Zamfara na da dimbin arzikin da ba kowa ke da shi ba a tarayyar Nijeriya, don haka za su iya yin amfani da arzikin su ci gaba da dogaro da kansu ba kamar yadda wasu ke yi wa yankin kirarin cima zaune ba.
Sai ya yi kira ga sauran Takwaroeinsa Gwamnoni da su hanzarta yin amfani da albarkacin karkashin kasa da Allah ya hore ma jihohinsu domin ciyar da kansu gaba, a daina dogara da sai Man Fetue ko kudin da ake samu daga Gwamnatin tarayya na rabon arzikin kasa.
Da tsari irin wannan za a iya cewa Gwamnan Jihar Zamfara Muhammadu Bello Matawallen Maradun na kokarin canza wa yankin arewacin N8jeriya suna musamman sunan da wadansu mutane ke kiran yankin da sunan cima zaune.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.