Home / Kasuwanci / Akwai Bukatar Gwamnati Ta Fadakar Da Mutane Game Da Haraji – Shehu Bello

Akwai Bukatar Gwamnati Ta Fadakar Da Mutane Game Da Haraji – Shehu Bello

Akwai Bukatar Gwamnati Ta Fadakar Da Mutane Game Da Haraji – Shehu Bello

Imrana Abdullahi

Shehu Bello, manaja Rigasa (A) kuma mai kula da karbar harajin bangaren motoci da ababen hawa masu zirga zirga a cikin karamar hukumar Igabi Jihar kaduna a tarayyar Nijeriya ya bayyana wa manema labarai irin halin da yake ciki wajen tattarawa Gwamnati kudin shiga a bangaren Mando da yankin Rigasa.

Shehu Bello ya shaidawa manema labarai irin wahalar da suke fuskanta wajen karbar kudin harajin ababen hawa musamman ga masu motocin haya na Bus da ke aiki a cikin gari gari saboda wadansunsu suna gani ne tamkar ba Gwamnati ce ta bayar da umarnin a karba ba.

“Wasu kuma suna ganin kamar wata kungiya ce take kokarin karbar kudi naira dari biyu a hannun masu motocin Bus da kuma naira dari daya daga hannun masu Baburan haya masu kafa uku, don haka irin matsalolin da muke fuskanta da wadansu masu motoci a game da karbar wannan kudin haraji hakika muna shan wahala domin artabun da ake yi bai dace a rika yinsa da su ba, don haka ya dace Gwmamnati ta tashi tsaye wajen tabbatar da ganin an waye wa jama’a kai”.

Bello ya ci gaba da cewa ba tsare hanya ake yi ba ana saboda babu tashar mota a bangaren karamar hukumar Igabi, misali a yankin unguwar Mando da Bakin ruwa duk babu tashar mota da za a yi amfani da ita domin ababen hawa su yi lodin jama’a a karbi kudi cikin natsuwa don haka sai a gefen titi, wannan lamarin aikin na yi mana wahala kwarai”.

“Suma jami’an tsaro suna koka maka cewa ba a yi masu bayani ba game da wannan lamari na karbar haraji, don haka Gwamnati nada aikin fadakarwa da ya dace ta aiwatar”.

Da man can an tsayar da sayar da rasidin biyan harajin ne saboda matsalar annobar Korona da ta gallabi duniya sai aka bayar da lokacin wata uku domin jama’a su huta yanzu kuma an dawo da sayar da wannan rasidin biyan haraji, saboda kamar yadda Jama’a suka Sani cewa Gwamnatin Jihar Kaduna na aiwatar da ayyuka ne da irin kudin harajin da take karba.

Sakamakon hakan muna kira ga wadanda ake karbar kudin nan a hannayensu da su kula su duba yanayin aiki da Gwamnati take ciki, a bayar da hadin kai da goyon baya ga Gwamnati ta samu damar yi wa jama’a ayyukan raya kasa da ya dace ta aiwatar.

Shehu Bello ya ce ” ni ma’aikaci ne na karamar hukumar Igabi mai kula da bangaren karbar harajin motoci masu aiki a gari gari domin in tabbatar nawa ake samu a kullum kuma a duk sati nawa ake hadawa duk zan hada in ba Gwamnati a rubuce, in sanarwa da dukkan shugabanni na ga yadda lamarin yake cewa ga abin da karamar hukuma ta samu duk da kudin ba karamar hukumar ake kai ma wa ba, ana kai wa Jiha ne amma duk da haka ina gayawa karamar hukuma ta san abin da ta samu za kuma abi a duba shin abin da na ce gaskiya ne ya zo Jihar ko bai zo ba.

Kuma za a duba sosai idan da wata matsala shin daga nine ko daga wurin masu karba ne a Jiha.

Ya kuma tabbatar da cewa duk masu yada wa cewa wai Gwamnati ba ta san da wannan abin ba ya dai yi ne domin kawai a tayar da zaune tsaye ya kuma kirkiri fitina kawai.

” Yakamat Gwamnati ta bayyanawa mutane ta kafofin yada labarai cewa an dawo da sayar da tikitin motocin Bus Bus da na Babura masu kafa uku da abubuwan hawa dai, duk wanda aka kama yana kokarin yin rikici da masu Sayarwa to za a dauki mataki a kansa saboda shi ya jawowa kansa duk abin da ya faru da shi, yin fadakarwar a kafafen yada labari zai sa kowa ya yi hattara kada wani abu ya faru da shi na bacin rai, ina ganin wannan shi ne mafita”.

Domin ba masu sayar da rasidin nan ne suka buga rasidin suke Sayarwa da jama’a ba, amma a koda yaushe hakan ake nunawa masu aikin sayar da rasidin nan.

” Duk lokacin da aka ba su tikitin nan sai mun san nawa aka ba su kuma guda nawa aka sayar kuma a nan karamar hukumar Igabi ba a fara sayar da tikitin sai mun tabbatar da komai mun kuma bayar da umarnin a fara Sayarwa.

Hakika mu dole ne mu godewa shugaban karamar hukumar Igabi Honarabul Jabir Khamis Rigasa bisa irin tsare tsaren da ya kawo a karamar hukumar na karbar haraji ba tare da an samu wata matsala ba, shi yasa a kullum bani nan bani can ina duba yadda ake sa

yar da wannan rasidi, in kuma mutum ya kawo matsala sai in tabbatar hukuma ta shigo ciki a samu zaman lafiya.

Ya dace dukkan hukumomin da suke karbar harajin nan su tanaji wani tsarin karewa duk masu tunkarar masu biyan kudin nan wani tsarin kiyaye masu mutunci koda za a samu wata matsala.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.