Home / Health / Akwai Bukatar Kiyaye Dokar Hana Fita A Kaduna – Kwamishina

Akwai Bukatar Kiyaye Dokar Hana Fita A Kaduna – Kwamishina

Kwamishinan kula da ma’aikatar Muhalli da albarkatun kasa na Jihar Kaduna Ibrahim Garba Husaini, ya bayyana batun kiyaye dokar da Gwamnatin Jihar kaduna ta kafa domin hana yaduwar cutar Covid – 19 da ake kira da Korona Bairus a matsayin abin da ya zama wajibi saboda kiyaye lafiya da dukiyar al’umma baki daya daga illar da ke tattare da cutar mai toshe numfashi, ya dai Bayyana hakan ne a lokacin zantawarsa da wakilinmu Mustapha Imrana Abdullahi da suka yi a Kaduna.

Garkuwa: Mun ga wani al’amari da ya faru a wannan wuri kan hanyar gidan Gwamnati a kan shatalai talan asibitin sojoji na 44

Kwamishina: To wannan al’amari dai kawai na fito ne domin inga irin yadda dokar zama a gida take gudana a nan cikin garin kaduna sai Naga wani mutum ya dauko Keke mai kafa uku (keke Napep), dauke da kayan masarufi tare da yan rakiya wanda hakan ya saba wa ka’idar da aka shimfida domin kiyaye wannan dokar zama a gida.

Amma sai fahimci cewa suna barin mutane haka kawai suna zirga zirgarsu ko’ina abin da ya sabawa doka, amma sai ga wasu sun makare babbar mai kafa uku da kayan abinci duk da a yau ba ranar da aka amince bace ayi zirga zirga ko mutane su fita.

Naga wani yana raka wanda ya dauko kayan a babur mai kafa uku ya ce wai shi dan Sanda ne kuma bashi da kayan sarki ko kayan aiki a tare da shi sai katin shaidar aiki cewa shi dan Sanda ne, ni kuma na ce me yasa suka fito. Kuma bamu san cewa lallai shi dan sandan bane na gaskiya sai na ce su bincika lamarin domin hana jama’a karya dokar da aka kafa ta hana yin zirga zirga a gari. Saboda akwai doka da ka’idar da aka kafa domin a tantance wadanda yakamata su fita da wadanda ba su da izinin fita.

Garkuwa: Ka fito kana zagaya wa shin yaya zaka bayyana wannan lamarin dokar hana fita yake tafiya?

Kwamishina: Akwai bukatar a kara ingantawa, jami’an tsaro akwai bukatar su kara ingantawa saboda an ba su cikakkiyar dama a bayyane da aka yi bayanin cewa ba wani mutum ba wani mutum da ke da damar yin zirga zirga sai wadanda suke yin aikin musamman kuma a bayyane ne karara aka ba su damar su fita.

Misali idan mutum ya dauko mara lafiya za shi asibitin 44 dole ne a bashi dama saboda yana kokarin kare rayuwar wani ne, Kuma mutane su Sani cewa wannan lokaci ba lokacin yin kudi bane don haka mutane su kiyaye doka da ka’ida, kowa yaba jami’an tsaro cikakken hadin kai da goyon baya domin su gudanar da ayyukansu

Garkuwa: Akwai batun rabon kayan tallafi da kai da kanka ka jagoranci rabon irin wadannan kayayyaki a wata karamar hukuma.

Kwamishina: To amma ka koma a kan wani al’amari daban, kana tambayata a kan batun rabon kaya. Koda yake zan iya yin magana kalma daya ko biyu. Gaskiya ne na jagoranci rabon kayan a karamar hukumar Kaduna ta Kudu, kuma a gaskiya mun yi rabon da tsari tare da tsare gaskiya da adalci mun kuma samu nasara, koda yake gaskiya an samu korafe korafe nan da can kasancewar ba zaka iya yin wani al’amari a karon farko ka same shi dari bisa dari dai dai ba. Amma mun yi kokari bakin yin mu kuma mutane da yawa sun yaba aikin namu sosai.

Mun kuma lura da korafe korafe mun rubuta su duk baki daya a wuraren da yakamata mu kara inganta aikin, nan gaba idan zamu yi sai mu kiyaye koda yake ba wanda zai iya gamsar da kowa sai Allah, amma dai a bakin iya abin da zamu iya mun inganta aikin sosai kuma an yi nasara kwarai.

Garkuwa: A game da korafin da su jami’an da za su kiyaye dokar nan a kan tituna da sauran wurare cewa suna bukatar a rika ba su wani dan alawus da zai taimaka masu kasancewa akwai iyalai da sauran bukatu.

Kwamishina: Hakika wannan ba hurumi na bane don haka ba zan iya amsa wannan tambayar ba.

Garkuwa: Mun gode

Kwamishina: Nima na gode.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.