Home / Labarai / TINUBU YA NADA GEORGE AKUME A MATSAYIN SAKATAREN GWAMNATIN TARAYYA

TINUBU YA NADA GEORGE AKUME A MATSAYIN SAKATAREN GWAMNATIN TARAYYA

Daga Imrana Abdullahi

Kamar dai yadda jaridar “Vanguard” ta rawaito cewa tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wasu muhimman nade – naden mukamai.

Ya zabi Sanata George Akume,a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Juma’a 2 ga watan Yuni, 2023.

Ga abubuwa bakwai game da Akume ku sani

Akume, wanda aka haife shi a ranar 27 ga watan Disamba, 1953, ɗan asalin gundumar Wannune Tarka ne na Jihar Banuwai.

A shekarar 1978 ya kammala karatunsa na digiri na farko a fannin zamantakewa a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo.  Haka kuma jami’ar ta ba shi digiri na biyu a fannin masana’antu da hulda da ma’aikata a shekarar 1986.

Akume ya zama Gwamnan Jihar Banuwai daga watan Mayu 1999 zuwa Mayu 2007 kuma a Jihar Banuwai shi ne gwamna na farko da ya yi wa’adi na biyu cikakku

Sannan, daga watan Yunin 2011 zuwa watan Yunin 2015, ya zama cikin jerin shugabannin  Majalisar Dattawa.

A dan takaitaccen lokaci da ya yi a majalisar dattawa tsohon Gwamnan ya taba zama shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji.

Sanata Orke Jev na jam’iyyar PDP ne ya kada shi a zaben 2019 domin zama dan  majalisar dattawa.

Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa, ya nada George a matsayin ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati a ranar 21 ga Agusta, 2019.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.