Home / Kasuwanci / AKWAI DIMBIN ARZIKIN MA’ADINAI DA NA JAMA’A A ABUJA

AKWAI DIMBIN ARZIKIN MA’ADINAI DA NA JAMA’A A ABUJA

DAGA IMRANA ABDULLAHI

An yi kira ga daukacin al’ummar duniya baki daya da su hanzarta zuwa babban birnin tarayya Abuja domin cin dimbin arzikin jama’a da kuma ma’adinai da ke shimfide a babban birnin.

Ministan Abuja Alhaji Muhammad Musa Bello ne ya yi wannan kiran lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a filin baje kolin kasuwar duniyar kasa da kasa da ke ci a halin yanzu jim kadan bayan kammala bikin ranar babban birnin tarayya Abuja da ake yi a kasuwar.

Ministan wanda ya samu wakilcin Mista Onah Joseph Ndubuisi , ya wakilta a wajen bikin ranar babban birnin tarayyar Abuja, ya ce akwai dimbin arzikin da kamfanoni da Gwamnatoci da sauran jama’a masu zaman kansu da suke a cikin duniya za su zo Abuja domin su samu.

“Muna fadakar da al’ummar duniya cewa akwai dimbin arzikin ma’adinai da na jama’a da ke shimfide a birnin tarayya, muna da ma’adinai da yawa da kamfanonin duniya za su yi amfani da shi”.

Mista Joseph, ya kara da cewa ko a kwanan baya sai da wani Ba Amurike mai dimbin arziki da duniya ta san da zamansa a kan kudi yazo birnin ya na neman samun amincewar Gwamnati na ya rika dibar ma’adanin “Lithium” ya rika fita da shi kasashen waje, amma aka gaya masa cewa sai dai a kafa masana’antar sarrafa ma’adanin a Najeriya”.

“Saboda mu a wannan kasar mun fi son abin da zai ba mutanen mu aikin yi don haka ba zamu bari a kwashi ma’adani saga wurin mu ba kai wata kasa sai dai a kafa masana’antar a nan Abuja don jama’ar mu su samu aikin yi Gwamnati kuma ta samu harajin da ya dace ta samu”.

Joseph, ya ci gaba da cewa akwai kuma tsarin sufuri a babban birnin tarayya da ke bukatar dimbin makudan kudi.

“Idan mutum na bukatar yin gine gine ne tun daga Otal har zuwa wadansu gine ginen zamani domin amfanin jama’a, akwai wadataccen fili a Abuja da har yanzu ba a yi amfani da rabin filin da ake da shi ba”.

“Ga kuma al’adu masu kyau da sauran abubuwan tarihi na gargajiya tare da dimbin jama’a da kuma harkokin Noma da ake bukata a duniya, don haka muke kira ga kowa a ciki da wajen Najeriya da ke bukatar zuba jari yazo babban birnin tarayya domin ya kwashi garabasa.

Akwai dukkan kwararru a kowa ne fanni ake bukata a cikin birnin tarayya da ke cikin birnin sakamakon kwararar jama’ar da ake samu a kullum zuwa Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Mista Onah Joseph, ya kuma yabawa KADCCIMA da ke shirya kasuwar duniyar kasa da kasa a Kaduna bisa yadda suke aiwatar da ita a duk shekara ba tare da gajiyawa ba

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.