Home / Big News / AKWAI INGANTACCEN TSARIN TSARO A KASUWAR DUNIYA TA KADUNA – FATIMA

AKWAI INGANTACCEN TSARIN TSARO A KASUWAR DUNIYA TA KADUNA – FATIMA

IMRANA ABDULLAHI
AN bayar da tabbacin samun ingantaccen tsarin kula da harkokin tsaron dukiya,lafiya da rayukan jama’a lokacin gudanar da cin kasuwar duniyar kasa da kasa da za a bude gobe Asabar a Kaduna.
Shugabar kwamitin yada labarai Hajiya Fatima Abdullahi da Kanar Jibril Hassan mai ritaya duk sun bayar da tabbacin samun ingantaccen tsarin tsaro a lokacin gudanar da kasuwar ta Bana da za a bude a gobe Asabar 26 ga watan Fabrairu 2022 zuwa ranar Lahadi 6 ga watan Maris 2022.
Kasuwar dai ta fara ne tun daga yau Juma’a 25 ga watan Fabrairu 2022, da ake saran dimbin jama’a daga ko’ina a fadin duniya za su halarta domin kawo kayayyakin amfanin al’umma daban daban.
Hajiya Fatima ta ci gaba da yin kira ga jama’a daga ko’ ina suke a fadin duniya da kowa yazo kansa tsaye ba tare da wata fargaba ba domin duk wani tsarin kula da lafiya, dukiyar al’umma a cikin da wajen wannan kasuwar duk an tanada, yadda aka fara gudanar da harkokin kasuwar lafiya za a kammala komai cikin Masara kamar yadda aka saba a kowa ce shekara.
“Gudanar da kasuwar duniya ba wani bakon al’amari ba ne mun saba aiwatar da shi a kowace shekara ayi cikin nasara da walwala kowa na jindadi da yi wa Allah godiya bukata ta biya nufi, tattalin arzikin kowa ya karu, Jihar Kaduna da Najeriya a matsayin kasa ta karbi bakuncin jama’a da kamfanonin da suka samu halartar cin kasuwar sun cimma bukatunsu na alkairi don haka a wannan shekarar ma an kara inganta tsarin da zai taimaki jama’a yan kasa da baki”, inji Fatima.
Don haka a madadin kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna, muna yin kira da fadakarwa ga kowa da suka hadar da Kamfanoni, Bankuna, cibiyoyin kasuwanci,yan kasuwa, ma’aikatu da bangarorin Gwamnati da masu bukatar zuwa kasuwar duniya da  azo a gudanar da duk harkoki da kulla hudda ta saye da Sayarwa da kasuwanci cikin natsuwa da kwanciyar hankali domin arziki ya ci gaba da inganta, kasancewar an yi tanajin dukkan abin da ya dace a samu na ci gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kwamitin tsaro na kasuwar Kanar Jibril Hassan mai ritaya, cewa ya yi a matsayinsa na shugaban kwamitin tsaro sun je wurin dukkan hukumomin tsaron da ke Jihar Kaduna kuma sun nemi taimakonsu sun kuma ba su tabbacin aiwatar da aikinsu kamar yadda ya dace don haka nema za a ga jami’an tsaro masu yunufan da farin kaya na boye duk a ciki da wajen kasuwar.
Saboda haka “muna ba dukkan mahalarta wannan kasuwa tabbacin samun ingantaccen tsaro don haka kada kowa ya samu wata fargaba komai zai ta fi cikin nasara tun daga farko zuwa karshen gudanar da kasuwar cikin ikon Allah ba matsala”.
Da wakilin mu ya zagaya kasuwar ya ganewa idanunsa irin yadda kamfanoni,Bankuna,ma’aikatu da hukumomin Gwamnati gami da yan kasuwa daga wurare daban daban suke Tururuwa suna sauke kayansu da suka halarci kasuwar tare da dukiyar ta su, wanda hakan ke bayar da tabbaci lallai komai lafiya an fara kalau za kuma a kammala cikin nasara.
Wakilin namu ya kuma kira wadansu bangarorin Gwamnatin tarayya duk sun bayar da tabbacin halartar kasuwar domin kuwa sun ce suna nan a kan hanya, wasu kuma sun shaida mana cewa tuni jami’ansu na cikin kasuwar ta duniya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.