Home / Labarai / Aliyu Waziri Dan Marayan Zaki Na Taya  Musilmi Murna Da Fatan Alkairi

Aliyu Waziri Dan Marayan Zaki Na Taya  Musilmi Murna Da Fatan Alkairi

Aliyu Waziri Dan Marayan Zaki Na Taya  Musilmi Murna Da Fatan Alkairi

Mustapha Imrana Abdullahi
Honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri, San turakin Tudun Wada da aka fi Sani da Dan marayan Zaki Kaduna ta Kudu cikin Jihar Kaduna, ya bayyana cewa fatan da yake yi wa daukacin al’ummar musulmi a wannan shagulgulan Sallah shi ne Allah ya karbi Ibadun da muka yi baki daya.
Aliyu Muhammad Waziri ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Kaduna ya ce “muna rokon Allah yafiya da Gafara tun daga wancan watan da ya gabata kafin Azumi har zuwa wannan da muka kammala Azumi lafiya Allah ya gafarta mana ya kankare mana duk wani laifin da muka Sani da wanda ba mu Sani ba, abubuwan da muka yi na alkairi Allah ya ninka mana ladan, idan ma akwai zunubin ya Sauya mana shi ya koma lada domin shi ne kawai keda ikon yin hakan ya kasance babu zunubin sai lada”.
Kuma ya kara da yin kira ga daukacin al’ummar Hausawa da Fulani a arewacin Nijeriya da kasar baki daya shi ne a zauna lafiya, mu ci gaba da yin addu’ar Allah ya kawar mana dukkan damuwar da muke ciki a kowane mataki, Allah ya kawo mana tsaro a kasa tare da yan kasar baki daya, ya karo mana hadin kai tsakanin malamanmu da shugabanninmu a dukkan matakai baki daya.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.