Home / News / Za Mu Samar Wa Manoma Taraktocin Noma Dubu 27 – Aliyu Waziri

Za Mu Samar Wa Manoma Taraktocin Noma Dubu 27 – Aliyu Waziri

Za Mu Samar Wa Manoma Taraktocin Noma Dubu 27 – Aliyu Waziri
….Mun Shiya samawa mutane miliyan 25 aikin yi
Imrana Abdullahi

 

Alhaji Aliyu Muhammad Waziri da ake yi wa lakabi da dan marayan Zaki ya bayyana irin kudirin da suke da shi na wayarwa da jama’a kai domin su rungumi harkar Noma ganin Gwamnatin tarayya da Gaske take yi wajen fuskar ciyar da Noman Gaba.

Na farko dai akwai wani shirin bunkasa harkokin Noma inda za mu shigo da motocin Noma (Tarakatoci) guda dubu Ashirin da Bakwai (27,000) da za a rabawa kananan hukumomi dari 528 inda a bisa bincike nan ne aka fi yin Noman, kuma kowace karamar hukuma an ware mata motocin Noman nan guda Hamsin (50) da za a kai wa manoma.

“Akwai shirin yin Noman zamani da za mu kawo a dukkan wadannan kananan hukumomin, muna da shirin samar da kayan Noma mai kyau da inganci duk da nufin taimakawa manoma, muna nan dai a kan shirin ko za mu samar da kayan Noman ne a wannan shekarar zuwa shekara mai zuwa kuma a kama aikin gadan gadan to, duk dai muna ta kokarin ganin hakan.

Aliyu Waziri, ya kara da cewa “motocin Noman nan ana kokarin kera su ne daga wata kasa sannan a kawo su cikin Jirgin Ruwa a sauke a Legas da Fatakwal, daga nan za a dauko su a kai Jihohin da za a rabawa manoman cikin Nijeriya da ake da kananan hukumomi dari 774 to, amma inda za a iya yin Noman shi ne aka tace aka fitar da guda dari 528 da za a ba kayan Noman da ya shafi na daya Taraktocin Noma, Irin shuka mai kyau, Takin Zamani na ruwa da na gari da aka saba da shi, domin a samu yabanya mai kyau da za ta bayar da amfanin Gonar da ake bukata.

Dan marayan Zaki ya kuma kara tabbatar da cewa a tsarin da suke kokarin yi ba maganar ba manoma bashi, “za mu nemi manomi ya nuna Gonarsa ba maganar mu danka wa wani mutum tarakta ba, domin Noman za a yi da gaske. Shi yasa za a nuna mana Gona ne Taraktar za ta yi ma mutum aiki ne a Gonar sannan mutum ya zo a bashi irin da yake bukatar ya shuka da kuma taki, famfon hannu na feshi tare da managin feshin da ake yin amfani da shi sai mutum ya dinga duba Gonar har lokacin yin girbin amfanin Gona”, Inji Aliyu Waziri.

A haka ne bayan an kwashe amfanin Gonar mutum zai dauki kashi Sittin ya ba mu kashi Arba’in (40) na amfanin Gonar da aka samu wannan shi ne tsarin da za mu bi, ba tsarin da ake cewa za a baka tallafin Noma mutum ya kara aure ko ya sayi mota ko dai wata hidimar gabansu daga baya kuma azo ana neman kudin ba a samu ba kamar yadda lamarin ya rika faruwa a can baya.

A can baya babban Bankin Nijeriya ya rika bayar da kudi idan mutum ya bayar da takardun abin da ya mallaka duk da hakan ma an yi ta samun matsala, kuma a hakan ma babban Bankin Nijeriya har yau bai samu kudin da ya bayar ga jama’a ba da sunan Noma koda kashi Ashirin da biyar ma ba a samu ba har yanzu, haka dai lamarin yake a dukkan shirye shiryen tallafin da Gwamnati ta fito da shi na ganin an Tallafawa jama’a sun tsaya da kafafunsu wato ta hanyar dogaro da kai duk lamarin ya zama fama ne kawai. Mu ba za mu ce mun zamarwa manomi wadanda za su tsaya a tsakiya ba tsakaninsa da Gwamnati babu wannan tsari, mu abin da muke yi shi ne mu samar da kayan Noma kowa ya koma Gona kawai domin ciyar da kasa da abinci, muna son koda ma’aikatan Gwamnati duk mun taimakemu kafin su ajiye aiki sun san su na da abin yi ba kamar yadda lamarin yake ba ma’aikaci kafin ya ajiye aiki gabansa na faduwa in ya ajiye aikin me zai yi kuma yaya rayuwa za ta kasance masa, hakika duk mun yi maganin hakan ta hanyar wannan tsarin samawa yan Nijeriya mutane miliyan Ashirin da biyar aiki, wannan shi ne tsari da manufar da muke da ita a halin yanzu.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.