Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Rahotannin da muke samu da sanyin safiyar nan daga wata majiyar iyalai na bayanin cewa Allah ya yi wa fitaccen dan siyasa a Jihar Zamfara da kasa baki daya Ambasada MZ Anka rasuwa.
Kamar dai yadda majiyar ta shaida mana cewa ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.
Kuma marigayin jigo ne a jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara da kasa baki daya.
Kamar dai yadda aka Sani cewa marigayi MZ Anka ne Mahaifin kwamishinar ma’aikatar lafiya ta Jihar Zamfara AI’sha MZ Anka