Related Articles
Allah Ya Yi Wa Ali Kwara Rasuwa
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da ke fitowa daga Jihar Bauchi na cewa Allah ya yi wa fitaccen mafaraucin nan da ke kama yan fashi da makami Alhaji Ali Kwara rasuwa.
Alhaji Lamara Garba Azare wanda ya bayyana cewa sun yi makarantar sakandare tare da marigayin a shekarar 1983 a makarantar GSS Gamawa, hakika ya san cewa Ali Kwara Azare ya Riga su kammala makaranta shekara daya amma abin da koda yaushe yake tunawa shi ne suna tafiya farauta tare da marigayin a kowane sati wato ranar Asabar tun daga lokacin Sallar Asuba sai sun kai Yamma sannan su dawo.
Zamu kawo maku karin bayani nan gaba..