Home / Labarai / Matawalle Ya Kafa Dokar Yin Bacci A Wajen Jihar Zamfara

Matawalle Ya Kafa Dokar Yin Bacci A Wajen Jihar Zamfara

Matawalle Ya Kafa Dokar Yin Bacci A Wajen Jihar Zamfara

Mustapha Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawallen Maradun, ya sanar da dokar yin hani ga duk wani shugaban karamar hukuma da Sarakuna da kada su sake a same su da rashin kwana a cikin Jihar Zamfara na tsawon watanni uku.

Gwamna bayyana dokar yin hani ga dukkan Sarakuna, shugabannin riko na kananan hukumomi da yin Bacci a wajen inda suke yi wa shugabanci tsawon watanni uku.

Gwamnan ya yi barazanar korar dukkan wanda aka samu da saba wannan umarnin.

Gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne a wajen taron wani daya domin tattaunawa a kan lamarin tsaro tare da Sarakuna, Malaman addini da shugabannin hukumomin tsaro da aka yi a dakin taro na gidan Gwamnati da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Kamar yadda ya ce daga yau sai yau babu wani Sarki ko mai jagorantar jama’a ko kuma shugaban rikon karamar hukuma da ke da wata damar kwana wani wuri ko dai dai da kwana daya ba a inda yake shugabanci ba.

“Dole ne ku zauna tare da mutanenku a koda wane lokaci domin a samar da mafita a game da matsalolin jama’a musamman na tsaro “.
Matawalle ya ce, don haka daga yau Haramun ne su rika kwana a wani wuri ba cikin inda suke yi wa shugabanci ba sai dai idan akwai wani kwakkwaran dalili.

Ya ce za a kawo takardar umarni zuwa nan da watanni uku inda ya kara da cewa duk wanda ya saba umarnin hakika a bakin aikinsa

Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa zai hukunta dukkan wanda aka samu da laifin taimakawa masu taimakawa ana lalata harkar tsaro a cikin Jihar.

“ A game da masu taimaka ma yan Ta’adda su rika lalata harkar tsaro a cikin Jihar kuwa, muna gaya masu lallai lamarin ya Isa domin an wuce wuri, ya isa haki ya Isa hakanan”.

“ zamu mayar maku da martani kan irin rashin imani da mugun abin da kuke aikatawa ta hanyar da baku yi tsammani ba”.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.