Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Dokta Ahmad BUK Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Dokta Ahmad BUK Rasuwa

Mustapha Imrana Abdullahi Kaduna
Allah ya yi wa sanannen Malamin addinin musulunci, Dokta Ahmad Ibrahim Bomba rasuwa.

Dokta Ahmad Ibrahim Bamba, sanannen Malamin addinin Islama da aka fi Sani da Dokta Ahmad BUK ya rasu ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Dansa mai suna Ahmad Muhammad Ahmad ne ya bayyana rasuwar Mahaifin nasa a cikin shafin Mahaifin na dandalin Sada Zumunta na fezbuk a ranar Juma’a.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana cewa za a yi Jana’izar mamacin a masallacin Darul Hadith, da ke unguwar Tudun Yol, a garin Kano da karfe 1.30 na ranar yau Juma’a.

Marigayin ya kasance Malami ne a jami’ar BUK da ke Kano a bangaren Koyar da larabci kafin ya ajiye aiki domin aikin yada addinin musulunci gadan gadan.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.