Bayanan da muke samu daga Jihar Jigawa da ke arewacin tarayyar Najeriya na cewa
Allah yayi wa Sardaunan Dutse Alhaji Bello Maitama rasuwa
Sanata Bello Maitama Sule ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Ya taba zama ministan ma’aikatar ciniki tun a zamanin NPN lokqcin mulkin marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari
Sanata Bello Maitama ya rasu ya na da shekaru 76 a duniya. Kafin rasuwar ta sa ya kasance Malami mai wa’azin addinin Islama da yake tafsiri a masallacin Gudansa da ke Unguwar Tarauni cikin birnin Kano.
Allah ya jiƙansa da rahama ya gafarta masa.