Home / News / Magaji Abdu Alhassan (Boss) Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Magaji Abdu Alhassan (Boss) Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

 

Bayanan da muke samu daga karamar hukumar Zariya a Jihar Kaduna na tabbatar da cewa Magaji Alhassan da ake yi wa lakabi da (Boss) ya fice daga cikin jam’iyyar PDP.
Ya dai bayyana ficewar ta sa ne a cikin wata takardar da ya rubutawa shugaban rikon jam’iyyar PDP na  mazabarsa ta Kwarbai cikin birnin Zariya, da kuma wata takardar da ya rubutawa shugaban PDP na kasa da ya aikewa babbar sakatariyar ta kasa da ke Abuja a wadata Plaza, inda yake shaida masa cewa ya bar mukaminsa na Ex- Officio mai wakiltar Jihar Kaduna.
Magaji Alhassan ya kuma aikewa ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna da kuma shugaban PDP na shiyyar Arewa maso Yamma da kuma shugaban rikon PDP na karamar hukumar Zariya duk ya aike masu da wannan takarda domin bayyana masu matakin barin jam’iyyar da ya yi.
Kuma duk mun ga takardar da ya aikewa dukkan wadannan shugabannin tun daga mazaba, karamar hukuma,jiha, shiyyar Arewa maso Yamma da kasa baki daya domin ya jaddada masu ficewar ta sa daga PDP, kuma munga shaidar da ke nuna tabbatar da cewa sun karbi takardar har wasu sun yi amfani da kan sarki na shaidar an karbi takardar wasu kuma shugabannin sun Sanya hannu tare da sunan wanda ya karbi takardar.
Ya zuwa yanzu dai bayanan da muka tattara na cewa a kalla sama da rukunin kungiyoyi sama da dubu uku ne suka canza sheka daga jam’iyyar inda duk sun fice daga PDP saboda yin biyayya da kuma nuna suna tare da Dallatun Zazzau Alhaji Dokta Muktar Ramalan Yero, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ne amma a halin yanzu ya fice daga cikin jam’iyyar ta PDP, inda sakamakon hakan dimbin magoya bayansa ke ficewa domin nuna goyon baya da kuma suna tare da mai gidansu a cikin PDP don haka suma sun fice.
Kamar dai yadda zaku iya gani ga takardun nan da Magaji Alhassan ya rubuta.

About andiya

Check Also

MAY DAY 2024: GOV. DAUDA LAWAL RENEWS COMMITMENT TO IMPROVE WELFARE OF ZAMFARA WORKERS

By; Imrana Abdullahi Governor Dauda Lawal reiterated his administration’s commitment to improving the well-being of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.