Home / KUNGIYOYI / AL’UMMA BADE SUN JA HANKALI DA KOKE GA SHUGABAN MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA

AL’UMMA BADE SUN JA HANKALI DA KOKE GA SHUGABAN MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA

A  yunkurin da jama’ar Mazabar shugaban majalisar Dattawa ta tarayyar Najeriya ke yi domin jawo hankalin shugaban majalisa wanda ya fito daga Jihar Yobe ya sa suka koka a cikin wata takardar da suka rabawa manema labarai domin yin nuni da kuma jan hankalin Dokta Ahmad Lawan, game da rabon mukamai da nufin a samu yin raba dai- dai a tsakanin al’ummar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Bade, BPF. da suka rabawa manema labarai.
 Al’ummar mazabar Bade da sauran jama’ar yankin mazabar dan majalisar Dattawa ta Yobe ta Arewa na kokawa da irin salon jagorancin shugaban majalisar dattawa Dokta Ahmad Lawan,PhD, GCON.
A batun gaskiya wannan matsalar ta kara tsauri ne lokacin da shugaban majalisar, Dokta Ahmad Lawan, tun lokacin da ya fitar da wani mai suna Ibrahim Babagana (YUREMA) a matsayin shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Bade.
Baki daya kowa ya Sani cewa zaben da aka yi wa Ibrahim Babagana, ba shi ne ya dace ya samu irin wannan ba na samun wannan kujerar,domin akwai wadansu jajirtattun mutanen da suka dade suna gabatar da ayyukan ciyar da harkar gaba da dadewa.
Saboda haka ne a wani bangaren dan za mu kira yin wariya daga salon jagorancin Dokta Ahmad Lawan, sun hada da al’ummar Bade su ne jama’ar da suka fi kowa yawa a karamar hukumar, hatta da kwamishinan ma daga cikin al’ummar Manga ya fito.
Na biyu kuma, shugaban jam’iyyar APC ma daga al’ummar Manga ya fito.Sai kuma kodinetan Tinubu / Shatima shima daga Manga yake. Shugaban kwamitin rikon da Dokta Ahmad Lawan ya zabo duk daga cikin al’ummar Manga yake shima, wato mai suna Ibrahim Babagana (Yurema)
 Da duk wadannan abubuwan na rashin samun dai- daito, za mu iya yin zargin cewa al’ummar Bade an yi masu wariya kenan? Wanda muke zargin Dokta Ahmad Lawan da kuma yaransa.
Ya dace shugaban majalisar Dattawa Dattawa Sani cewa, dukkan wani karfi da ikon mulki daga Allah yake kuma ya na bayarwa ne ga duk wanda yaso a lokacin da yaso.
Duk wani kokarin da Lawan ke yi da gangan da kokarin dakile yan siyasa masu tasowa daga cikin al’ummar Bade da Katuzu ba zai taimaka masa ya ci gaba da zama a kan kujerar mulki ba har abada.
Saboda haka ne muke yin kira ga Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, CFR da shima ya duba irin wannan matsalar rashin samun raba dai dai din, ya kuma yi kokarin tabbatar da dai daito a tsakanin jama’ar Jihar musamman a karamar hukumar Bade.
Mai girma Gwamna ya dace ya ci gaba da tunawa cewa mutanen Jihar Yobe sun amince da shi ne suka bashi wannan jagorancin, wanda wani lamari ne daga Allah kuma duk wani mutum zai tsaya a gabansa a ranar bayar da sakamako abin da ita ko shi wato mace ko Namiji ya aiwatar.
Ga shugaban majalisar Dattawa kuma idan ya na son dawo wa da Soyayya da hadin kai na al’ummar Bade, dole ne sai ya kawar da duk son zuciya da wasu bukatun siyasa musamman a wajen zaben wadanda za su rike ofishin siyasa da Ofisoshi.
Idan har an samu aiwatar da hakan, hakika muna tabbatar da cewa za a samu hadin kai da fahimtar Juna a tsakanin al’umma
Kungiyar ci gaban al’ummar Bade sananniya ce a game da batun samar da zaman lafiya da ci gaban kasa baki daya.
Kuma kungiya ce da ke kokarin kare muradun mutanen ta, saboda haka ne muke cike da kokarin bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga shugaban majalisar Dattawan Najeriya Dokta Ahmad Lawan,muna kuma shawartarsa da ya yi kokarin samar da yin dai – daito a matsayin abin da ya dace ya ba muhimmanci, a cikin al’ummar Bade.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.