Home / Big News / Ambaliyar Ruwa : An Yi Asarar Sama Da Biliyan 2 A Jihar Kebbi

Ambaliyar Ruwa : An Yi Asarar Sama Da Biliyan 2 A Jihar Kebbi

Imrana Abdullahi
Alhaji Sani Dododo, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ne a Jihar Kebbi ya bayyana irin asarar da aka yi sakamakon matsalar ambaliyar ruwan sama a Daminar Bana da ya ce asarar ta kai sama da biliyan biyu.
Alhaji Sani Dododo ya ci gaba da bayanin cewa hakika an samu mummunar ambaliyar ruwan sama da ya mamaye Gonakin shinkafa da yawan filin ya kai fadin hekta sama da dubu Arba’in da biyar, amma idan aka hada da yawan wuraren da aka samu ambaliyar na Gonakin Masara da inda ruwan ya mamaye gidaje za a iya samun yawan fadin hekta sama da dubu Hamsin.
Ya dai Lissafa wurare daban daban a wadansu kananan hukumomin da abin ya shafa inda ya ce lamarin ya taso ne tun daga kan iyakar Jihar Kebbi da Sakkwato ya kwararo zuwa karamar hukumar Arugungu, Bagudo, Arewa, Ingaski da sauran wurare da dama.
Ya kara da cewa a halin yanzu lamarin ya Sanya wadansu mutane tilas sai da Gwamnati ta Tsugunnar da su aka sama masu wadansu abubuwan kayan rayuwa.
An kuma samu rasa rayuka na wasu mutane biyu da kuma wadansu mata 10 da suka shigo Jirgin kwalekwale suka samu matsala da a halin yanzu an samu Gawar mutane 3 ana nan kuma ana ci gaba da neman sauran wadansu.
Dododo ya kuma ce sun samu zagayawa tare da Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Abubakar Atiku Bagudu sun kuma ganewa idanuwansu yadda matsalar ambaliyar ta faru da wuraren da ta mamaye, abin da ya bayyana da bashi da dadin gani ko kadan.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.