Home / KUNGIYOYI / An Bayyana Rikicin Kudancin Kaduna Da Cewa Ya Haifar Da Talauci, Lalacewar Tattalin Arzikin Yankin

An Bayyana Rikicin Kudancin Kaduna Da Cewa Ya Haifar Da Talauci, Lalacewar Tattalin Arzikin Yankin

 Imrana Abdullahi
Yayan Kungiyar musulmi yan asalin Kudancin Kaduna karkashin kungiyar Muslim Youth Foundation Of Southern Kaduna ne suka bayyana hakan a karshen taron tattaunawar da suka gudanar a Kaduna.
A cikin wata sanarwar da suka fitar bayan kammala taron tattaunawar a kan yankin Kudancin Kaduna, Kabiru Muhammad, wanda shi ne shugaban kungiyar ya tabbatarwa manema labarai a Kaduna cewa.
“Rikicin da ake yi a yankin Kudancin Kaduna ya haifarwa da yankin Dimbin matsalolin da suke haifar da illolin ci bayan yankin masu yawa”.
“Kowa ya san wannan yanki da Noma da kuma Kiwo, Noman Citta, Tamba, Acca da sauran kayan Noma da yawa amma duk wadannan abubuwa sun yi karo da cikas sakamakon matsalar rikicin da wannan yanki ke fama da shi na kabilanci, bambancin addini da wadansu bambance bambance da dama”.
Ya ci gaba da cewa babu mai zuwa yankin domin yin kasuwanci saboda rashin zaman lafiya wanda hakan ci baya ne kwarai.
Kabiru, ya kuma yabawa irin yadda Sarkin Atyap ya dauki matakan zaman lafiya a yankin domin sai da zaman lafiya ne kawai za a samu ci gaban da ake bukata.
Sai dai a waje daya kuma sun soki lamirin irin furicin da kungiyar SOKAPU suka yi na sukar matakin da Sarkin Atyap ya dauka domin a samu zaman lafiya, abin da suka ce bai dace ba ko kadan.
Yan kungiyar Musulmi yan asalin Kudancin Kaduna sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da aka yi a lokacin da aka samu rikice rikice a tun shekarar 1980 da Gwamnatin Jiha ta kafa kwamitoci a lokuta daban daban duk lokacin da aka samu wani rikici.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.