- Ambaliyar Ruwa A Jega
Imrana Abdullahi
A yau Mutanen Garin Jega suntashi acikin Alhini na Iftila’in Ambaliyar ruwa Wanda yayyi sanadiyar rasa mahallin da Dukiyoyin wasu gami da Abinci.
Amadadin kungiyar Move on Kebbi State muna Mika sakon jaje ga Yan uwan mu mutanen garin Jega bisa ga wannan iftila’in na Ambaliyar ruwa wayanda sukayi sanadiyar rushewar gidajen mutane da kuma hasarar dukiyoyi da Abinci.
Dafatar Allah ya mayar musu da Alkhairi, Allah ya hore musu abin da za su mayar da mahalinsu acikin sauki. Allah ya Kara tsare gaba.
Muna Kira ga Gwamnati da kuma masu Hannu da shuni da su taimaka da gudarmuwarsu ga wannan Al’umma musamman talakawa daga ciki don ganin cewa sun samu saukin gyara mahalinsu sun koma gidajensu da suda iyalansu.
Allah ya Kara tsare mu da dukko miyagun kaddarori.
Abubakar Na’amare Jega
(Jagaban M. Jega and Chairman, Move on Kebbi State)