Home / Ilimi / Aminu Dantata ya Dauki Nauyin mutane 100 Domin Yin Karatu A Jami’ar Al-Istiqama Ta Sumaila

Aminu Dantata ya Dauki Nauyin mutane 100 Domin Yin Karatu A Jami’ar Al-Istiqama Ta Sumaila

Aminu Dantata ya Dauki Nauyin mutane 100 Domin Yin Karatu A Jami’ar Al-Istiqama Ta Sumaila
Mustapha Imrana Abdullahi
Alhaji Dokta Aminu Alhassan Dantata ya dauki nauyin dalibai guda dari (100) da za su yi karatu kyauta a sabuwar jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila. Daliban dai za su yi karatu kyauta karkashin tsarin bayar da tallafin karatu wanda shi Alhaji Aminu Dantata ya dauki nauyi.
Alhaji Dantata ya bayyana cewar, a cikin irin gudunmawar da yake baiwa harkar Ilimi ya dauki nauyin dalibai guda dari, wanda yace dukkansu zasu kasance ‘ya ‘yan talakawa ne domin taimaka musu gina da kuma inganta rayuwarsu.
Dantata ya yi godiya ga Allah da ya sanya aka zabi Farfesa Salisu Shehu a matsayin mataimakin shugaban jami’ar na farko a cewarsa, Farfesa Shehu mutumin kirki ne mai kula da addini da kuma taka tsantsan.
Da yake maida jawabi, a madadin kwamatin gudanarwa na jami’ar Honarabul Kawu Sumaila  ya yi addu’ah a kan Allah ya yalwata masa arzikinsa ya kuma saka masa da alheri ya tsawaita rayuwarsa cikin yalwar arziki da wadata tare da koshin lafiya.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.