Home / Labarai / Babu Batun Yin Sulhu Da Yan bindiga, Masu Satar Mutane – Aruwan

Babu Batun Yin Sulhu Da Yan bindiga, Masu Satar Mutane – Aruwan

Babu Batun Yin Sulhu Da Yan bindiga, Masu Satar Mutane – Aruwan
Mustapha Imrana Abdullahi
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya kara jaddada batun cewa babu maganar yin sulhu da yan bindiga ko masu satar mutane suna karbar kudin fansa.
Kwamishina Samuel Ariwan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta bbc hausa.
Aruwan ya ce wannan matsayi ne da Gwamnatin Jihar ta dauka kamar yadda Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ya bayyanawa duniya tun farko.
“Ta yaya za a yi sulhu da mutanen da suke sace jama’a su na karbar kudin fansa kuma su shiga garuruwa su kashe mutane su kwashe masu Dukiya, sun dauke jama’a sun karbi kudinsu haka kawai kuma su yi wa mata fade, sai ace za a dai- daita da su kamar yaya”, inji shi.
Ya kara da cewa don haka Gwamnati na nan a kan matsayar da ta cimma tun farko.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.