Home / KUNGIYOYI / Zamu Tunkari Kalubalen Da Ke Gaban Mu Gab Da Gaba – Kwamared Ayuba

Zamu Tunkari Kalubalen Da Ke Gaban Mu Gab Da Gaba – Kwamared Ayuba

Zamu Tunkari Kalubalen Da Ke Gaban Mu Gab Da Gaba – Kwamared Ayuba
Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Muhammad Suleiman, ya bayyana wa yan majalisar dokokin Jihar Kaduna cewa uwar kungiyar ta kasa ta ba su umarnin lallai su tunkari wannan bala’in da ke gaban ma’aikata gaba da gaba.
Kwamared Ayuba Suleiman ya ce batun albashin da wani dan majalisar wakilai ya bijiro da shi a majalisar hakika zai zamarwa ma’aikata wata gagarumin matsala don haka dole sai an tunkare shi gaba da gaba ba tare da gajiyawa ba.
” A yanzu haka ma da yaya ma’aikaci ke gudanar da rayuwarsa balantana an fito da wani tsari kuma can daban”.
Yayan kungiyar dai wato gangamin ma’aikata a Jihar Kaduna ne suka je majalisar dokokin Jihar Kaduna domin nuna rashin amincewa da tsarin da ake neman kawowa da sunan Albashi, ” ba mu amince ba kuma ba za mu amince da wannan tsarin ba shi ne sakon”, inji yan kwadagon.
Kuma yayan kungiyar ta kwadago sun kasance a cikin rana su na rera wakar kungiyar domin samun kwarin Gwiwa suna rangaji suna gaba suna yin baya suna tausawa Dama suna tausawa hagu suna tunanin kwatar yanci kawai.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.