Home / Labarai / An Bayyana Halin Cutar Korona Da Ake Ciki A Matsayin Jarabawa Daga Allah

An Bayyana Halin Cutar Korona Da Ake Ciki A Matsayin Jarabawa Daga Allah

Imrana Abdullahi

Shugabar kungiyar wa’azi da yada addinin Musulunci IMWON ta kasa Malama Rabi’ah Shmad Sufuwan, ta bayyana hakuri, Juriya da komawa ga Allah a matsayin abin da ya dace a yanayin da ake ciki na Covid – 19 da ake kira Korona bairus.
Ta bayyana hakan ne lokacin da ta ce ganawa da manema labarai a Kaduna
Malama Rabi’ah Sufuwan ta ci gaba da cewa abin da ake bukata a tsakanin al’umma Maza da Mata cikin yanayin Korona bairus da ake ciki shi ne hakuri, juriya da ganin girman Juna a tsakanin magidanta Maza da Mata.
Ya dace maza su Sani cewa ba fa mata ne suka kawo wannan cutar ba da har wasu suke kasa yin hakuri da yanayin iyali har sai a rika kaiwa yara duka sakamakon bacin rai, duk baki daya hakuri da Juna ne kawai magani har Allah ya ba jama’a ikon cin jarabawar da ake ciki.
Malama Rabi’ah ta kuma yi kira ga daukacin mata musulmai da su yi koyi da irin halayen Matan Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) domin yin hakan zai kara inganta yanayin zamantakewa a tsakanin maza da matansu.
“Hakika hakuri da juriya tare da ganin mutuncin Juna ana girmama kowane bangare tsakanin Maza da Mata ma’aurata zai taimakawa rayuwar zaman aure da tafiyar zamantakewa baki daya, kuma zai taimakawa wajen cin jarabawar da Allah madaukakin Sarki ya Dorawa duniya sakamakon Korona bairus”. Inji Rabi’ah Sufuwan.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.