Home / Kasuwanci / An Bude Baje Kolin Kanana Da Matsakaitan Masana’antu A Kaduna Da Akwa Ibom

An Bude Baje Kolin Kanana Da Matsakaitan Masana’antu A Kaduna Da Akwa Ibom

An Bude Baje Kolin Kanana Da Matsakaitan Masana’antu A Kaduna Da Akwa Ibom
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban hukumar da ke kula da kanana da matsakaitan masana’antu a tarayyar Nijeriya Dokta Dikko Umar Radda ya kara jaddada kudirin Gwamnatin Nijeriya karkashin Muhammadu Buhari a kan taimakawa harkar bunkasa masana’antu a kasa baki daya.
Dokta Dikko Umar Radda ya bayyana hakan ne a wajen taron bude baje kolin kanana da matsakaitan masana’antu na wannan shekarar da aka yi a filin kasuwar baje kolin kasa da kasa da ke Kaduna.
An dai shirya bake kolin ne dai tare da hadin Gwiwar ma’aikatar kimiyyar kasuwanci ta Kaduna da hukumar SMEDAN.
Dokta Dikko Radda ya ce an wannan shekarar an tsara bude baje kolin ne a jihohi biyu da aka zaba na Kaduna da Akwa Ibom, an kuma zabi a kaddamar a Kaduna.
Za a yi tsawon kwanaki biyar ne daga 3 ha watannan zuwa Bakwai domin mahalarta baje kolin su samu daga manyan kamfanoni da hukumomin Gwamnati da suka hada da Bankuna domin samun muhimman bayanan da ya dace su samu a kan yadda za su bunkasa sana’o’insu a ciki da wajen Nijeriya ta yadda al’amuran kasuwanci da abubuwan da suke samarwa za su bunkasa jama’a su amfana.
Mahalarta sama da 90 ne suka halarta da za su ci gaba da samun ingantattun muhimman bayanai daga Bankin kula da yadda ake fitar da kaya kasashen waje daga Nijeriya sai kuma hukumar NAFDAC, Bankin Manoma,hukumar Ma’adinai ta kasa da sauran wadanda suka halarta domin yi wa kanana da matsakaitan masu yin sana’o’i cikakkun bayanai.
Dokta Radda ya ci gaba da cewa a wannan sati ne Gwamnati ta kaddamar da tsarin bayar da Tallafi ga Direbobin Keke Napep, Achaba da Direbobi da masu Kurar ruwa domin rage radadin cutar Korona, kuma za a ba su kudi naira budu 30,000 ne ga dukkan wanda ya cika sharuddan bayar da tallafin da ake yi a yanar Gizo da kowace Jiha za ta samu yawan mutane dubu 4,500.
Shugaban ya ci gaba da cewa a game da batun wannan Tallafi na Korona babu wanda zai iya yi wa wani hanya sai dai wanda ya cika ta hanyar yadda aka fitar da ka’ida a yanar Gizo.
Sharudda uku kawai ake bukata da suka hada da mutum ya kasance dan Nijeriya, mutum ya kasance  yana da rajistar kungiyar da zai cika a karkashinta sai ka lambar asusun ajiyar Banki kamar yadda dokar kasa ta tanadar kuma duk wanda ya rika cikawa kafin a samu ka’idar mutane dubu 4,500 a kowace Jiha banda Legas da Kano saboda yawan jama’arsu an kara masu yawan jama’ar da za su samu tallafin.
Shugabanna SMEDAN ya kuma kai ziyara ga shugaban Kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna kuma sun tattauna batun Sanya hannu a yarjejeniya a tsakanin bangarorin biyu da za a aiwatar na gaba.
A wannan hoton za a iya ganin Dokta Dikko Umar Radda rike da itacen yin Turaren wuta  sai Manajan SMEDAN na Jihar kaduna Alhaji Badamasi lokacin da suka halarci rumfar wadda take hada Turaren wuta mai samar da kamshi.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.