Home / News / An Yi Kira Ga Jama’ar Bakori Su Kiyaye Doka Da Ka’ida

An Yi Kira Ga Jama’ar Bakori Su Kiyaye Doka Da Ka’ida

An Yi Kira Ga Jama’ar Bakori Su Kiyaye Doka Da Ka’ida
Mustapha Mahmud Kanti Bello, Kwamishina ne na raya karkara a Jihar Katsina ya bayyana gamsuwarsa da irin yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta raba kayan zabe a kan lokaci domin zaben cike gurbi na Dan majalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar karamar Hukumar Bakori.
Mustapha Kanti Bello ya shaidawa manema labarai a garin Bakori cewa hakika hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ( INEC) ta raba kayan zabe a kan lokacin da ya dace, saboda haka muke yin kira ga daukacin ma’aikatanta a duk inda suke su ci gaba da riko da wannan hali na yin aiki tukuru domin kasa ta kara inganta.
“Hakika hukumar zabe ta yi aikin rabon kayan zabe a kan lokaci, don haka muke yin kira ga jama’a su yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana a samu nasarar da kowa ke bukata wajen ci gaban kasa”.
Kwamishina Kanti, ya ce al’amuran zabe a Nijeriya suna kara inganta kasancewar a can baya ana yin zabe ne ta hanyar yin amfani da tsohon tsarin yin zabe amma a halin yanzu al’amura sun ci gaba ana amfani ne da tsari na ci gaban zamani, wanda hakan na nuni da cewa nan gaba za a samu ingancin yin zabe kamar yadda kowace kasa da ta ci gaba ke amfani da shi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafartawa tsohon Dan majalisar Bakori da ya rasu.

About andiya

Check Also

Borno: Zulum delivers 556 capital projects in two years 

  Borno State Governor, Prof. Babagana Umara Zulum has led his administration to the delivery …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *