Home / Kasuwanci / An Bude Kasuwar Duniya Ta Kaduna

An Bude Kasuwar Duniya Ta Kaduna

 

…Ba Mu Yin Bacci Saboda Halin Da Kasa Ke ciki – James Barka

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an ci gaba da bunkasa tattalin arzikin Jihar Kaduna da kasa baki daya duk da irin matsin tattalin arzikin da ake fama da shi Jagororin da ke kokarin ganin a kowace shekara an samu aiwatar da cin kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna a wannan shekarar ma ta 2024 an kaddamar da bikin bude kasuwar karo na 45 da ake yi a harabar matsugunnin kasuwar da ke Rigachikun kan titin Kaduna zuwa Zariya.
Ga daya daga cikin jami’an kamfanin Dangote nan ya na mikawa manyan bakin da suka halarci babban taron bude kasuwar duniyar kasa da kasa a Kaduna a yau 24 ga watan Fabrairu, 2024

A wajen babban taron bude kasuwar ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Jihar Kaduna da suka hada da babban wakilin shugaban majalisar wakilai ta kasa Dokta Abbas Tajuddeen, Iyan Zazzau, wanda ya samu wakilcin Honarabul Shu’aibu James Barka shugaban kwamitin kula da harkokin kasuwanci na majalisar da kuma Babban Sakataren ma’aikatar cinikin Jihar Kaduna Sale Anchau da dukkansu suka yi muhimman jawaban kara karfin Gwiwa da kuma kokarin ci gaba da harkokin kasuwanci, masana’antu da kuma ci gaban Noma a kasa baki daya.
Sai dai a a jawabinsa wakilin shugaban majalisar wakilai ta kasa Honarabul Shu’aibu James Barka, ya yi kira ga daukacin yan Najeriya da su ci gaba da yin hakuri kamar yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa da yan Najeriya cewa shima ya na jin zafin irin halin da suke ciki don haka a kara ci gaba da hakuri.
“Hakika ta yaya za mu iya yin Bacci bayan mutanen kasa na cikin wani hali, kuma mune da wakilan jama’a da kuma muke tare da su a koda yaushe”.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.