Home / Labarai / An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta
Daga Imrana Abdullahi
Shugaban gamayyar kungiyoyin da suke fafutukar taimakawa jam’iyyar APC na kasa Farfesa Kailani Muhammad ya yi kira ga daukacin yayan jam’iyyar a ko ina suke a fadin tarayyar Najeriya da su ci gaba da zama yan uwan Juna ta hanyar hadin kai da taimakekeniya da nufin ciyar da kasa gaba.
Hakika kokarin da yayan jam’iyyar APC keyi ne ya haifarwa da jam’iyyar samun cikakkiyar nasarar da ake gani a fagen mulkin da ake yi karkashin jam’iyyar.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Farfesa Kailani Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin APC na karamar hukumar Igabi da suka kai masa gaisuwar Sallah a gidansa da ke Unguwar Rigasa a cikin garin Kaduna a arewacin tarayyar Najeriya.
Farfesa Kailani Muhammad ya bayyana farin cikinsa da ganin irin yadda yayan jam’iyyar suka hada kansu. musamman wajen aiwatar da ayyukan jam’iyya lamarin da ke haifarwa jam’iyyar samun ingantacciyar nasara a koda yaushe a duk fadin karamar hukumar Igabi baki daya.
Farfesa Kailani Muhammad ya ci gaba da bayanin cewa hakika ya fara gamsuwa da irin yadda ake daukar shawarar da yake bayarwa musamman da “na je wajen shugaban jam’iyyar APC na kasa na kuma bashi shawarar da ya ta fi Jihohi ya zauna da shugabannin jam’iyyar nan da sauran mambobin ta koda wadanda aka ba ta wa rai a lallashe su a ba su hakuri domin su zo a ci gaba da tafiya tare, saboda kamar yadda kowa ya Sani duk mutum dan Adam ya na da rana musamman ma a ranar zabe koda mutum daya ne sai a rissina mashi a samu cin zabe domin kuri’a daya na iya cin zabe kuma ya ce za a yi a kafa kwamiti kwamiti abi mutane ko’ina suke”.
Farfesa Kailani Muhammad ya kuma ja hankalin shugabannin jam’iyyar da suka fito daga dukkan mazabun karamar hukumar Igabi da duka kawo masa ziyara cewa su tashi tsaye domin babban aiki na gabansu na su je su zagaya dukkan mazabu a samu wadanda aka ba ta masu a ba su hakuri. Koda yake a halin yanzu an fara aikin horas da wadanda za su yi wa yayan jam’iyya rajista ta yanar Gizo don haka muna fata hakan zai yi aiki ya haifar da bunkasa da ci gaban jam’iyya, amma dai an san akwai wadanda aka yi wa rajista a kowa ce Mazaba kuma ana ci gaba da yin rajistar don haka koda za an zo lokacin yin rajista a yanar Gizo kawai sai ku mika wadannan sunayen domin kuma azo ayi maku horaswar domin kun tabbatar da cewa a mazabun mu ga wadanda muka samu ya zuwa yanzu sai a shigar kawai .
Sai ya yi godiya ga shugabannin jam’iyyar da suka zo daga mazabu na karamar hukumar Igabi bisa wannan ziyarar da aka kawo mashi.
Ya kuma jawo hankalin su da cewa idan tafiyar APC ta yi kyau hakika sune idan kuma ta baci nan ma sune saboda haka zagayawannan da shugabannin keyi a halin yanzu sai sa jama’a kowa ya kara farkawa musamman a tsakanin shugabannin jam’iyya don haka duk wani abu ya bangaren Farfesa idan za a yi a Abuja za a yi magana a kawo mutane ayi da su.
” Hakika mutane na cikin wahala ko an ki ko an so amma idan an zo za a yi gyara sai an shiga cikin irin wannan halin don haka muna fatan a wannan shekarar an samar da tsare tsare da dokokin da za su fitar da Najeriya daga cikin wannan halin da take ciki. Kiran mu dai ga jama’a shi ne a kara hakuri.
Sai kuma ya yi kira ga Dokta Usman Lukman da cewa a lokacin da yake a cikin su ya fito ya fadi abin da yake yi wa jama’a duk da kasancewarsa mataimakin shugaban jam’iyya a Arewa, me Lukman ya yi na fitar da mutanen Arewa daga cikin halin da suke ciki? na biyu ya Sani fa bai fi su son El-rufa’I ba domin kanin su ne Allah ya jikan yayansa Aliyu Ahmed Rufa’I tare ake da shi aka yi komai. Kuma da ya fito a shekarar 2015 din nan ba inda ba a shiga ba ana kamfe an zabe shi haka ma a shekarar 2019 ma duk sun zabe shi saboda haka kudin nan da aka ce an bankado ba karamin kudi ba ne biliyan dari 423 ba fa wanda ya ce shi barawo ne amma an ce ga abin da aka ce ana nema majalisar Jihar Kaduna sun zauna idan ya san ba shi da laifi sai yaje ko ya ta fi Efcc ya ta fi da dukkan takardun sa baki daya ya kuma yi bayani dalla dalla har ya kammala bayanin kudi naira biliyan 432 aga lallai ya yi aikin shikenan.
“Shi kuma Lukman ya Sani ba shi da kowa fa har yake cewa wai zai tara jama’a a Kaduna. Ya dace ya Sani cewa fa Kaduna Nufawa ne suka kafa Kaduna in bai Sani ba layin Shaba, Magajin Gari da titin indifenda, Kasuwa da siteshin duk wani gida da ke nan Nufawa ne don haka kada ya sake ya yi wasa da mu, Ga Zage zagi, katsinawa da kanawa duk suna tare da mu ni fa a unguwar makwarari na tashi a cikin birnin kano tun a 1960 gudan mu ba nisa da Jakara ba wanda zai gaya mana komai a nan Kaduna har ya rika cewa binciken da ake yi wa El-rufa’I a daina wai har ana cewa idan ba haka ba Gwamna Uba Sani ba zai ci zabe ba 2027 shi Allah ne? don haka ya daina wargi ya kuma daina surutu sai an zo an rike gaskiya da Amana a kasar nan

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.