Home / News / An Dakatar Da Micheal A Auta, Bashir I Aliyu Da Ibrahim Sidi Bamalli A Jam’iyyar Lebo

An Dakatar Da Micheal A Auta, Bashir I Aliyu Da Ibrahim Sidi Bamalli A Jam’iyyar Lebo

Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon irin matsalar da ke neman dabaibaye jam’iyyar Lebo reshen Jihar Kaduna a tarayyar Najeriya biyo bayan irin yadda wasu daga cikin yayanta aka tabbatar da sun halarci wani haramtaccen taro a Jihar Bauchi da sunan jam’iyyar Lebo ya sa shugaban jam’iyyar na Jihar Kaduna kiran taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.
Taron da shugaban jam’iyyar Alhaji Auwal Ali Tafoki ya kira shugabannin, Sakatarori da shugabannin mata an yi taron ne a cikin garin Kaduna wanda har wanda ya tsayawa jam’iyyar takarar Gwamnan Jihar Kaduna wato Jonathan Asake ya samu halarta tare da dimbin yayan jam’iyyar daga kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna.
Bayan an kammala yi wa mahalarta taron jawabi daga shugaban jam’iyya da kuma dan takarar Gwamna Jonathan Asake sai shugaban jam’iyyar Lebo na karamar hukumar Jaba Ruben Tukura ya tashi a cikin taron ya ambata gabatar da kudirin amincewa da dakarar da wadancan mutane uku da suka halarci haramtaccen taron Jihar Bauci da sunan jam’iyyar Lebo, sai kuma shugaban jam’iyyar Lebo na karamar hukumar Kaduna da Arewa Shamsudeen Garba Waziri ya amince da kudirin da Ruben Tukura ya gabatar da Dakatar da mutane uku jiga – Jigan jam’iyyar a kasa da Jihar Kaduna.
Hon Bashir Idris Aliyu, ya tsaya takarar mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna ne da kuma Alh. Ibrahim Sidi Bamali, da ya tsayawa jam’iyyar takarar Sanata a yankin shiyya ta daya da kuma jigo a jam’iyya Injiniya Michael Ayuba Auta duk taron ya amince da takatar da su uku baki daya.
Hakazalika a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar a Jihar Kaduna Idris Yusuf da ya karanta da kansa a gaban taron a matsayin abin da taron ya cimma duk ya jaddada matakin da aka dauka tun farko na Dakatar da mutanen uku.
Idris Yusuf ya karanta cewa biyo bayan irin yadda jam’iyyar ta gano cewa wadansu mutane sun yi wani haramtaccen taron masu ruwa da tsaki a ranar 3 ga watan Mayu,2023, alhalin a can Abuja ana gabatar da taro makamancin wannan da ya hada da daukacin masu ruwa da tsaki daga Jihohin Najeriya 34 karkashin jagorancin karkashin Barista Julius Abure.
Kuma muna tabbatarwa da yayan jam’iyyar Lebo a ko’ina suke a cikin fadin duniya cewa masu yin wancan haramtaccen taro na yi ne domin kawai a haifar wa da kokarin dan takarar shugaban kasa Peter Obi da yake yi a kotun sauraren karar zaben shugaban kasa a yanzu haka, wanda mu Allah yasa mun gano don haka muka dauki wannan matakin dakatarwa ga mutane uku.
Hazakalika mu a matsayin mu na halartattun yayan jam’iyyar Lebo masu kishin ta da yi mata aiki Dare da Rana Safiya da Maraice muna tabbatar wa da duniya cewa ba mu tare da wani kirkirarren bangare na karkashin wani mutum Lamidi Apapa, ba mu ba wannan tafiya Sam.
Kuma ba mu tare da wancan haramtaccen taron da aka yi a Jihar Bauci karkashin Lamidi Apapa
Sa’Annan ba mu amince ba da duk abin da aka ce an cimma wa a wajen taron Bauci da Lamidi Apapa ya jagoranta ba.
Kuma mu a iya sanin mu da kuma amincewar mu da shugaban jam’iyyar Lebo a Jihar Kaduna shi ne Alhaji Auwal Ali Tafoki don haka duk mai ikirarin cewa wai shi shugaba ne laifi ne mai girma da yake aikatawa.
Kamar dai irin yadda takardar ta ce dukkan abin da aka cimma a wannan gagarumin taron masu ruwa da tsaki da aka yi za a aikawa hedikwatar Sakatariyar ta kasa da dukkan wadanda ya dace a aika masu domin tabbatar da bin doka da oda.
Taron dai ya gudana ne a ranar 6 ga watan Mayu, 2023 a Kaduna.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.