Home / Labarai / An Dakatar Da Wazirin Zazzau Ibrahim Aminu

An Dakatar Da Wazirin Zazzau Ibrahim Aminu

An Dakatar Da Wazirin Zazzau Ibrahim Aminu
Imrana Abdullahi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta Dakatar da babban kansila a masarautar Zazzau wato wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu.

Takardar dakatarwar da babban kansilan an aike masa da ita ne daga ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya a ranar Alhamis 19 ha watan Nuwamba, 2020.

 

Takardar dalatarwar na dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar, Musa Adamu a madadin kwamishinan ma’aikatar Jafaru Sani.

 

Wazirin Zazzau dai yana daya daga cikin masunzaben Sarki a masarautar Zazzausauran masu zaben Sarkin  hudu sun hada da Limamin Gari – Alhaji Dalhatu Kasim, Limamin Kona – Muhammad Dani Aliyu, Makama Karami – Alhaji Muhammad Abbas, da fagacin Zazzau – Alhaji Umar Muhammad dukkansu ba a san makomarsu ba tukuna.

Alhaji Ibrahim Aminu wanda ya shugabanci zaben sabon Sarkin Zazzau, Waziri, Limamin Kona, and Limamin Juma’a sun zabi Iyan Zazzau, yayin da Fagacin ya zabi Yarima sai Makama karami ya zabi Turaki.

 

Amma Gwamnan Jihar Kaduna yaki ya yi aiki da abin da suka yi a matsayinsu na masu zaben Sarkin sai ya zabi Ambasada Bamalli, duk da masu zaben Sarkin Sarkin su zabe shi ba.

Nadin da aka yi ya haifar da batun zuwa kotu, kuma za a fara shari’ar a ranar 11 ha watan Disamba, 2020 a babbar kotun Jihar Kaduna.

“ Kuma batun shari’ar ta hada da mutane 11 da suka hadavda masu zaben Sarki biyar (5). Kuma su masu zaben Sarkin sun dauki lauyansu kuma dukkansu sun sa hannu a matsayin da suke”.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.