Home / KUNGIYOYI / Al’ummar Igbo Za Su Gyara Nijeriya – Barista Christ Nnoli

Al’ummar Igbo Za Su Gyara Nijeriya – Barista Christ Nnoli

Imrana Abdullahi

 

Barista christ Nnoli, shugaban kula da walwala da jin dadin al’ummar Igbo na Jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban Igbo na Jihohin arewa 19 ya bayyana cewa idan an ba al’ummarsa jagorancin Nijeriya za su ciyar da kasar tare da al’ummarta gaba kamar yadda aka sansu da bunkasa ko’ina suka samu kansu.

 

Barista Christ Nnoli ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ziyarar da al’ummar Igbo suka kai domin yin ta’aziyyar marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a gidansa da ke Kaduna.

Al’ummar Igbo kenan lokacin da suka kawo ziyarar gaisuwar ta’aziyya gidan marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa a layin Aliyu Turaki

 

“Hakika ba zamu mance da irin rayuwar Abdulkadir Balarabe Musa ba saboda ya yi rayuwar da ta bayyana a fili cewa kowa nasa ne babu wani bambanci saboda haka rayuwarsa ta amfani kowa a daukacin Afrika da Nijeriya baki daya”.

 

Barista ya ci gaba da cewa “duk inda al’ummar Igbo suke zaune ba shakka akwai zaman lafiya domin su yan kasuwane da ke kokarin ciyar da kasa gaba ta hanyar saye da sayarwa”.

 

“Saboda shi marigayi Balarabe Musa ya yi maganar cewa ya dace aba al’ummar Igbo suma su yi shugabancin Nijeriya domin su bayar da irin ta su gudunmawar wajen ciyar da kasa gaba, don haka a shekarar 2023 aba su dama suma su taka ta su rawar, kasancewarsu suna nan a ko’ina a Nijeriya suna harkar ciyar da kasa gaba”.

A dama shugaban kungiyar al’ummar Igbo Barista Christ Nnoli tare da dan marigayi Balarabe Musa Sagir Balarabe Musa

 

Barista christ ya ce in ana son wanda ya fi son Nijeriya to al’ummar Igbo ne domin suna son a ci gaba ta zama daya ta yadda Nijetiya za ta zama kasar da ta fi kowace a nahiyar Afrika da duniya baki daya.

 

Duk inda mutanen Igbo suke za su tabbatar an gyara wurin to, kasancewar Igbo na son kasa ne yasa duk inda suke suna gyara wurin kuma ingantaccen gyara, saboda haka in an bar Igbo zai gyara Nijeriya wannan yasa marigayi Abdulkadir Balarabe Musa ya ce bai kamata a bar Igbo a baya ba.

 

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.