Home / Labarai / An Fasa Ofishin Alkalin Babbar Kotun Da Ke Shari’ar Sarkin Zazzau A Dogarawa 

An Fasa Ofishin Alkalin Babbar Kotun Da Ke Shari’ar Sarkin Zazzau A Dogarawa 

 Imrana Abdullahi

Biyo bayan yadda aka fasa ofishin mai shari’a a babbar kotun da ke Shari’a kan nada sabon Satkin Zazzau da iyan Zazzau Bashar Aminu ya kai a halin yanzu bayanai daga birnin Zazzau sun tabbatar mana cewa tuni mai gadin kotun na can yana amsa tambayoyi game da faruwar lamarin.

 

A daren ranar Talata ne wasu bata-gari da ba a san ko su wanene ba, suka fasa ofishin babban Alkalin kotun Dogarawa, Mai Shari’a Kabir Dabo, wanda yake shari’a tsakanin sabon sarki, Ahmed Bamalli da Iyan Zazzau, Bashir Aminu.

Sai da bata-garin suka fasa kotun, tukunna suka samu damar shiga har ofishin babban alkalin. Bata-garin sun yi kaca-kaca da wasu takardu, sun kuma kwashe kayan da alkalin yake amfani da su idan zai zauna a kotu, da wasu abubuwa da har yanzu ba a gama tantancewa ba.

 

Wakilin jaridar Aminiya ya bukaci tattaunawa da magatakardan kotun, mai suna Jafaru, amma abin ya ci tura, inda ya ce yanzu dai ba zai iya magana da shi ba, har sai ya tuntubi mai gidansa.

 

Wannan hari da aka kai a Kotun ya jefa jama’a Jihar Kaduna musanman na yankin mazaɓar Zazzau cikin taraddadi da shiga ruɗani a kan dalilin faruwar hakan.

Wasu na ganin harin bai rasa nasaba da shari’ar da ta gudana tsakanin Sarkin Zazzau Bamalli da Iyan Zazzau Bashar Aminu.

 

Duk da faruwar wannan lamari dai za a iya cewa Shari’a Mace ce da ciki ba a san abin da za ta haifa ba.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.