Home / Labarai / AN GA WATAN AZUMIN RAMADANA A KADUNA DA KATSINA

AN GA WATAN AZUMIN RAMADANA A KADUNA DA KATSINA

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Bayanan da muke samu daga Jihar Kaduna da Katsina sun tabbatar da cewa an ga watan Azumin Ramadana a garuruwan Daura, Katsina Funtuwa da cikin garin Kaduna.
Kamar yadda kuka karanta a cikin wannan labarin na cewa an ga watan Azumin Ramadana a garuruwa da yawa da suka hada da Kaduna da Daura.
A garin Funtuwa jama’a sun ga watan Azumin a gaba na mai rubuta wannan labarin wanda kuma daga baya na je wurin da ake kallon watan na ganshi.
Sai kuma a garuruwan Daura da cikin garin Kaduna wadanda suka gani sun tabbatar mana da cewa an ga jinjirin watan.
Da fatan Allah yasa mu dace kamar yadda muka gan shi lafiya ya sa mu dace da kuma kammala Azumin lafiya ya datar da mu dukkan alkairan da ke cikinsa amin.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.