Home / Big News / An Gabatar Da Mai Unguwa, Tsohon Kansila Gaban Kotu Saboda Zargin Sayar Da Tiransifoma

An Gabatar Da Mai Unguwa, Tsohon Kansila Gaban Kotu Saboda Zargin Sayar Da Tiransifoma

An Gabatar Da Mai Unguwa, Tsohon Kansila Gaban Kotu Saboda Zargin Sayar Da Tiransifoma
 Imrana Andullahi
Jami’an yan sanda sun gurfanar da wani mai unguwar Kwangila tare da tsohon kansilan kula da harkokin Noma da kula da Gandun Daji a karamar hukumar Sabon, Yusuf Garba bisa zargin karkatar wa da sayar da na’urar rarraba hasken wutar lantarki ( Tiransifoma) ta mutanen unguwar kwangila da ke karamar hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.

Wadanda ake Zargin an dai gabatar da sune a gaban kotun Majistare ta 1,  da ke Chediya unguwar GRA Sabon Gari, Zariya bisa zarginsu da hada baki a aikata abin da ya sabawa ka’ida da sata da karbar kayan da aka sace.

Dan Sanda mai gabatar da kara ASP Jubril Aliyu ya shaidawa kotu cewa laifin ya sabawa sashe na 59,271, 294 da sashi na 302 na dokar fenal Jihar kaduna.

Jubril ya ce a ranar 29, ha watan Satumba, 2020 ne shugaban karamar hukumar Sabon Gari ya gabatar masu da koke a kan wadannan mutane da ake wa zargi.

Ya kara da cewa wadanda ake wa zargin sun hada baki da sayar da wata na’urar rarraba hasken wutar lantarki ta mutanen unguwar kwangila ga wani mutum da ba a san shi ba wanda kuma a yanzu ya tsere an dai sayar masa da na’urar ne a kan kudi naira dubu dari hudu (400,000).

Mai gabatar da karar ya ci gaba da cewa su dai wadanda ake karar sun karkatar da kudin ne domin amfanin kansu.

Wadanda ake karar sun ce su ba su yi laifi ba a bisa zargin da ake yi masu.

Lauyan da ke kare su Mista Nasiru Abubakar ya rubutawa kotu neman Belin wadanda ake kara, amma mai gabatar da karar yaki amincewa da neman belin

Mai shari’a Cif Majistare, Mista Lamido Abubakar ya bayar da belin wadanda ake kara sai dai ya bayar da sharuddan belin kamar haka cewa wadanda ake kara kowannensu zai bayar da kudin ajiya naira dubu dari Takwas ( 800,000) za su bayar da kudin ajiyar ne ga kotu tare da gabatar da mutanen da za su tsaya masu mutum biyu da ke zaune a inda hurumin kotun yake.

An dage zaman sauraren karar ne zuwa ranar 29, ha watan Satumba, 2020 domin saurare.

mun samu wannan ne a nnn kaduna

 

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.