Home / Big News / Muna Bukatar Matashi A Matsayin Shugaban Kasa – Makeri

Muna Bukatar Matashi A Matsayin Shugaban Kasa – Makeri

Muna Bukatar Matashi A Matsayin Shugaban Kasa – Makeri

Imrana Andullahi
Wadansu matasa a tarayyar Nijeriya karkashin Inuwar matasa masu hangen zama shugabannin Gobe ( Visionaty Young Nigerian Leaders Initiative) sun yi kira ga daukacin matasan tarayyar Nijeriya da su farka domin karbar shugabancin kasar.
Honarabul James Makeri ne ya jagoranci wadansu matasa da suka zo cibiyar manema labarai reshen Jihar kaduna inda baki daya ta bakinsa suka jaddada yin kira ga matasan Nijeriya da su hanzarta yin shirin karbar ragamar shugabancin kasar a shekarar 2023 mai zuwa.
Makeri ya bayyana cewa kungiyarsu na a kowane irin mataki a baki dayan kananan hukumomin Nijeriya guda 774 kuma sun yi kyakkyawan shirin kasancewa a kowane akwatin zabe da ke mazabun kasar baki daya.
Sai dai ya yi kira ga masu yin kiran a fito domin yin fito na fito ta hanyar juyin juya hali domin karbar mulki da cewa shi tare da dukkan mabiya tafiyar da suke kafawa a Nijeriya ba su tare da irin wannan kiraye kirayen sam baki daya.
” Saboda babu wata hukima a rika kiran jama’a zuwa yin juyin juya hali domin ana son a karbi shugabancin kasa”, inji makeri.
Matsan sun kuma yi kiran cewa babu wata hukima a wajen yin karin kudin man fetur da kuma wutar lantarki musamman su a ganinsu “Babu wani tsari mai kyau ta fuskar samarwa mutane hasken lantarki, saboda mutane da yawa ba su ma da koda mita mai nuna yawan wutar da suka sha ko suka yi amfani da ita, to ta yaya za a yi wa mutane karin kudin wutar lantarki”. Inji James Makeri.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.