Home / Labarai / An Hana Yin Hawan Sallah A Masarautun Jihar Kano Biyar

An Hana Yin Hawan Sallah A Masarautun Jihar Kano Biyar

Imrana Abdullahi
Majalisar zartaswar Jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana hanin yin hawan Sallah a duk fadin Jihar.
Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya shaidawa manema labarai a lokacin wani taron manema labarai da ya yi a Kano.
Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa hakika bayan duba a tsanake da Gwamnatin ta yi ta hana yin hawan Sallah a dukkan masarautu biyar da ake da su a Jihar Kano baki daya.
“Dukkan sarakuna za su yi Sallah ne a masarautunsu tare da bin ka’idar hana yaduwar cutar Korona kamar yadda suke a tsare”.
Saboda haka ake yin kira ga daukacin jama’a da su kiyaye dukkan ka’idojin da aka shimfida a tsarin hana yaduwar cutar Korona.

About andiya

Check Also

Sokoto APC supporters take over major streets for Aliyu Sokoto’s victory

  By Suleiman Adamu, Sokoto   It has been jubilation all through by thousands of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.