Home / Labarai / Yan Bindiga Sun Sace Mata 17 Tare Da Dimbin Dukiya

Yan Bindiga Sun Sace Mata 17 Tare Da Dimbin Dukiya

 Imrana Abdullahi
Wasu mutanen da ke garin Zakka a karamar hukumar Safana cikin Jihar Katsina sun koka game da irin yadda Yan Bindiga suka zagaye garin a ranar Lahadin da ta gabata inda suka kwashe mata 17 da suka hada da yan mata da matan aure tare da wata karamar yarinyar da suka saki bayan sun ta fi da su cikin daji.
Mazauna wannan gari na Zakka sun tabbatar da cewa yan bindigar sun zagaye garin na Zakka ne da misalin karfe 12 : 58 na daren Lahadin da ta gabata amma sun kwashe tsawon lokaci inda suka kai karfe 2: 44 na dare kafin su fita da dimbin dukiyar da suka kwashe.
” A lokacin wannan garin dai yan bindigar sun bi gida gida inda suka balle shaguna da bincike gidajen mutane, sula kwashe shanu da yawa tare da tafiya da mata 17.
Sai dai mutanen garin sun bayyana wa manema labarai cewa mata 4 sun samu kubuta bayan da suka ta fi da su sai kuma wasu da suka kubuta lokacin da jami’an tsaro suka tare yan bindigar,” majiyar dai ta shaida mana cewa a yanzu a kalla sun tafi da mata guda tara da suka hada da mata yan mata har da na aure”.
“A bare dai an kawo mana jami’an tsaro da suka zagaye garin Zakka wannan mataki ya taimaka domin yan bindigar ba su samu zuwa garin ba,a yanzu wadanda suka rage a garin sai dai mutanen da ke da nauyi da yawa saboda yawan iyali sai kuma marasa karfi amma duk wanda zai iya motsawa ya amu wata dama a wani wuri duk tuni sun bar garin tun da dadewa”.
” Ko a lokacin wannan harin ma mazaje duk sun bi kan katanga domin tsira da rayukansu inda suka shiga daji wanda hakan ya ba yan bindigar damar daukar mata 17 tare da dimbin dukiya”.

About andiya

Check Also

Za Mu Kakkabe Yan Ta’adda, Bola Tinubu Ya Tabbatarwa Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na kawo ƙarshen matsalar ’yan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.