Home / KUNGIYOYI / An Kaddamar Da Bayar Da Horo Ga Jami’an JTF A Kaduna

An Kaddamar Da Bayar Da Horo Ga Jami’an JTF A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin harkar tsaron lafiya da dukiyar jama’a sun inganta rundunar hadin Gwiwa ta JTF reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin Shehu Usman Dan Tudu ta kaddamar da bayar da horo na kwanaki biyar ga jami’anta dari biyar (500), da nufin samun kwarewa su bayar da gudunmawarsu wajen samar da ingantaccen tsaro a cikin al’umma.
Shugaban gamayyar kungiyar jarumai da Gora na Jihar Kaduna Shehu Usman Dan Tudu, ya shaidawa manema labarai cewa jami’an nasa za su samu horo ne irin wanda ake yi wa jami’an Yan Sanda a kwalejin horas da Yan Sanda da ke cikin garin Kaduna na tsawon kwanaki biyar, wanda hakan zai taimaka kwarai ta fuskar sanin aiki a cikin al’umma.
“Mun samu irin wannan horo a can baya tun da muka samu amincewa daga ofishin shugaban rundunar Yan Sanda na kasa, kuma hakika mun ga amfaninsa domin dukkan jami’an mu da suka halarci wannan horaswar duk sun canza kuma suna aiwatar da aiki kamar yadda ya dace domin amfanin kasa da al’ummarta baki daya”, inji Dan tudu.
Ya ci gaba da cewa muna umartarku da ku zamo ma su ladabi da biyayya a lokacin samun horon da zaku je a babbar kwalejin horar da jami’an Yan Sanda, saboda amfani al’umma baki daya.
A wajen taron kaddamar da fara bayar da horon na kwanaki biyar da aka yi a makarantar Firamare ta titin Maiduguri da ke cikin garin Kaduna, an mika daukacin jami’an da za su halarci taron ga mai aikin bayar da shawara mai su na Osijons International a kan harkokin tsaro wanda shi ne matsayin Gada tsakanin gamayyar kungiyar jarumai da Gora da kuma rundunar Yan Sanda ta kasa domin samar da horon ga jarumai da Gora.
Shehu Dan tudu ya bayar da tabbaci ga dimbin jami’an na sa cewa su tsaya su mayar da hankali ga aikin horon da ake ba su domin babu wata damuwar da za su samu saboda hatta abinci ma ba matsala ba ne a tsawon lokacin da za su kwashe ana ba su horo a kwalejin Yan Sandan.
Jami’in hulda da jama’a kuma mai magana da yawun gamayyar kungiyar jarumai da Gora Malam Sanusi Surajo, jan kunnen mahalartar taron horaswar ya yi da cewa su tabbatar da tsare dukkan wata ka’idar da za a shimfida masu wajen bayar da horon.
“Kuma kada kowa ya sake ya sayi kayan jami’an Yan Sanda wato yunifom domin babu wata hujjar yin hakan”, inji Surajo.
A nasa jawabin mai aikin bayar da shawarar Osinjons International gargadi ya yi wa mahalarta samun horon da cewa ya na ba su tabbaci cewa a karshen wannan samun horo kowa zai samu nasarar fitowa a matsayin wani mutum na daban ba kamar yadda yake a can baya ba.
Ya kuma gargade su da kada su sake su nuna dabi’ar shaye shaye ko neman shan wani abu a baki dayan lokacin samun horon
Ya ce yadda ya dauki amanarsu har suka shiga kwalejin bayar da horon ta Kaduna da ikon Allah babu wani abu da zai samu kowa sai alkairi.
A cikin wadanda za su samu horon sun hada har da wani Fasto da ya yi kira ga yan uwansa malaman addini da su shigo JTF domin bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban al’umma.
Jami’an JTF din da za su samu horon sun hada da Maza da Mata inda muka tattauna da wata mace da ta ce hakika ta na kiran daukacin Mata da su shigo kungiyar domin bayar da gudunmawarsu al’umma ta samu tsaron lafiya da ci gaba tare da karuwar arziki.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.