Daga Imrana Abdullahi Kaduna
A kokarin ganin an aiwatar da ayyukan Gwamnati kamar yadda ya dace musamman ta fuskar bayar da Izinin yin Gini, hukumar KASUPDA ta Jihar Kaduna karkashin jagorancin Dokta Abdurrahman Yahya ta kaddamar da sabon Tambarin hukumar domin ba jama’a tabbacin samar da sabuwar hukuma ce mai aiki tukuru domin jin dadin al’umma baki daya.
Kamar yadda shugaban hukumar masanin harkar Gini Dokta Abdurrahman Yahya ya shaidawa jama’a cewa a yau ranar 9 ga watan Disamba 2024 Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Kwamared Sanata Uba Sani ta amince a kaddamar da wannan sabon Tambari (Logo) wanda za a rika yin amfani da shi a dukkan takardun da ke Hukumar a matsayin alama ta hukumar.
Sai dai shugaban ya ce za a ci gaba da yin aiki da sauran takardun da ke dauke da tsohon Tambari har sai sun kare sannan a ci gaba da yin amfani da wannan sabon da nufin samar da ciyar da al’umma gaba.
An dai kaddamar da wannan sabon Tambarin ne a wajen babban taron jin koke – koken jama’a karo na biyu da hukumar ke shiryawa a kowane watanni Uku domin ba al’ummar damar gabatar da korafinsu ga dukkan mai korafin