Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Shitu Adamu Bargaja, Talban Isa kuma shugaban Zamfara wa,Sakkwatawa da Kabawa mazaunan Kano da Jigawa, sannan shi ne shugaban Kungiyar hadin kan Hausa da Hausawa ta duniya reshen Najeriya, ya bayyana cewa kaddamar da sababbin shugabannin kungiyar da aka yi alamace na tafiyar za ta yi kyau.

Alhaji Shitu Adamu Bargaja, Talban Isa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da sababbin shugabannin a Kaduna.
Ya ce manufar tafiyar shi ne ci gaban Hausawa da masu jin Hausa a duk inda suke a duniya duk inda bahaushe yake da mai jin Hausa ta yadda za a samu ci gaban da kowa ke bukata

Shitu Bargaja, ya kuma ce ya na yin kira da babbar murya ga dukkan Bahaushe a duk inda yake ya nuna al’adarshi ta Hausa kasancewar Hausa a kullum kara habbaka take ta na ci gaba.
THESHIELD Garkuwa