Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Bello Shehu Mai Gada, Shugaban kungiyoyin da ke fafutukar hadin kan arewacin Najeriya wato ( arewa qualiation of Youth) ACY, ya bayyana cewa an kafa kungiyar ne musamman domin ta taimaki yan arewa musamman matasa saboda a yanayin da ake ciki a halin yanzu matasa sun kasance a yanayi na kara zube.
Don haka ne muka ga ya dace a samar da wata tafiyar da za ta kasance kamar mabudi ga matasa su yi wa kansu yaki har a kai ga an ci gajiya ko ribar dimokuradiyyar da ake yi a kasa a halin yanzu.
“Hakan ya sanya aka yi tsayuwar daka aga cewa cikin jihohin nan Goma sha Tara aka hada kan matasa ta yadda za a nema masu hakkinsu a koda yaushe duk abin da ya dace ayi masu a tabbatar an yi masu a tare da jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A game da batun irin yadda kungiyarsa mai tarin jama’a sama da dubu sittin da biyar ke goyon bayan Tinubu a halin yanzu sai Honarabul Mai Gada ya kada baki ya ce Alhamdulillahi, mu a ganin mu ya zama dole ne fa ga duk dan arewa na kwarai ya ga ya yi tsayin daka sai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake cin zabe a shekarar 2027 mai zuwa da yardar Allah domin idan aka duba akwai ayyukan da tsohon shugaban kasa marigayi Umar Musa Yar’aduwa ya fara amma sai ga shi Allah bai bashi ikon ci gaba ba kowa ya san abin da ya faru sai ayyukan suka tsaya sai Allah ya kawo shugaba Buhari ya fara ayyuka kamar irin aikin hanyar Abuja zuwa Kano, aikin samar da tashar wuta ta Mambila da aikin hako Man fetur na Kwolmani ga su nan dai amma sai ayyukan suka tsaya, hakan ta sanya wannan kungiya ta yi magana kuma shugaban kasa ya saurare ta kuma ya amince da cewa za a yi wadannan ayyukan”.
Saboda haka ne muke tabbatar wa da jama’ar arewacin Najeriya da kasa baki daya cewa ya na da kyau Bola Ahmed Tinubu ya koma domin ayi mana wadannan ayyukan har da karin wasu nan gaba ta yadda kasa da al’ummarta za su ci gaba.
Haka zalika a game da irin ci gaban da yankin arewa ya samu a halin yanzu a lokacin wannan shugabanci na Tinubu kuwa sai ya ce idan aka duba a mukaman Gwamnati akwai muhimman mukamai da yan arewa ne ke taka rawa, haka idan an kalli tun daga nan Jihar Sakkwayo a garin Illela za a yi aikin titin Jirgin kasa daga Illela zuwa Legas bayan nan kuma akwai ayyukan ci gaba da babu wata jihar da ba a sanya irin wadannan ayyukan ba domin kasa ta ci gaba, sai nan Sakkwato kuma idan aka dubi damar da mai girma shugaban kasa ya ba su sai hamdala ga Allah domin a zamanin sauran Gwamnatocin da suka gabata ba a samu hakan ba saboda haka ne muke ankarar da jama’a domin kada a samu matsala kowa ya tsaya tsayin daka ya tabbatar Tinubu ya sake komawa a karo na biyu.
Sai ya yi kira ga yan arewacin Najeriya da su gujewa rudin yan adawa kasancewar Bola Tinubu mutum ne da duk abin da yake yi sai da yan arewa a cikin mulkinsa idan aka duba ministoci kamar na Gona da tsaro da mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro baki daya Dan arewa ne don haka muke Jan hankalin jama’a da a koda yaushe su rika saurare da karanta ainihin labaran abin da ke faruwa a kasa don gujewa jita jita kasancewar mun san Shugaban kasa mutum ne kwararre, haziki da ba zai yarda da duk abin da zai kawo wa Najeriya koma baya ba”, Inji Bello Mai Gada.