Home / Uncategorized / An Karrama Shaikh Zakariyya Usman 

An Karrama Shaikh Zakariyya Usman 

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Sakamakon aiki tukuru wajen karantar da dimbin al’umma ilimin addinin musulunci da kuma bunkasa tattalin arzikin arewacin Najeriya da kasa baki daya ya sa kungiyar yan jarida masu wallafa jaridu da mujallu ta Arewa mai suna “Arewa Publishers Forum” karkashin Dokta Sani Garba suka Karrama Shaikh Zakariyya Usman da nufin sauran jama’a su yi koyi da ayyukan ci gaban al’umma da Shaikh Zakariyya Usman yake aiwatarwa.

Jim kadan bayan Karrama shi a cikin jawabinsa da ya gudanar Shaikh Zakariyya Usman ya karantar da duniya kamar yadda ya saba da niyyar kowa zai samu babban rabo a duniya da lahira kamar haka.

Inda Shaikh ya ce “Babban abu mai muhimmanci shi ne mutum ya kara neman sanin Allah sannan ka bauta masa dogara gare shi sannan a  bauta masa kuma mutum ya zamanto duk abin da yake yi da gaske mutum yake yi domin Allah gaskiya ne, Manzon Allah gaskiya ne kuma addinin musulunci gaskiya ne, ranar tashin kiyama gaskiya ne sannan kuma ayi hakuri saboda sai da hakuri ake cin nasara.

Shaikh Zakariyya Usman ya kuma fadakar da al’umma cewa mutum ya zama ya na da ikilasi kasancewar ikilasi ne mai daukar ayyuka zuwa sama zuwa wajen madaukakin sarki Allah, ta hanyar tauhidi kuma kadaita Allah abu ne mai muhimmanci kwarai a rayuwar jama’a kasancewar Allah ne wanda ba a yin tarayya da sunayensa don haka sai dai a bauta masa shi kadai kada a hada shi da dukkan komai.

Wannan a lokacin da aka Karrama babban mai ba Gwamnan Jihar Kaduna sanata Uba Sani shawara a kan al’amuran addini Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman lokacin da ya karbi lambar karramawar daga Arewa Publishers Forum

Shaikh kuma ya ci gaba da fadakar da al’umma a kan horon da rikon Amana kada mutum ya ci Amana, amma kuma su kasance masu yarda da Kaddara, sannan Allah na son godiya, saboda haka ne shaidan ya ce ba zan bari bayinka su gode maka ba a Kan abin da ka yi masu ba sai Allah ya ce ba zaka samu iko a kan bayi na ba, ikilasi na da muhimmanci kwarai da gaske sannan istigfari kasancewar dukkan yan Adam masu kurakurai ne amma fiyayyen ku shi ne wanda ke yin istigfari don haka a rika neman tuba.

Shaikh ya kara da cewa ya dace mutane su rika yin goyi da Manzon Allah Annabi muhammadu SAW da ya kasance mai yi wa Allah godiya ta hanyar yin Istigfari domin wani hadisi ya ce ya na yin tuba sau saba’in sai kuma na uku a cikin rukunnan musulunci Zakka saboda haka ya dace a san cewa rukunnan musulunci biyar na da muhimmanci a koda yaushe. Aikin hajji da kuma Azumi kun ga a kwai lokacin da nisabin Zakka yake a naira dubu Bakwai (7000) saboda a can baya lokacin mulkin Buhari da Ediyabon na farko kudin Najeriya ya yi daraja kuma kudin Sadaki bai wuce naira daya ba,amma a yanzu kudin nisabin Zakka sai kudin ka ya kai naira miliyan biyu da dubu dari biyu (2.2) kuma idan mutum kudinsa bai kai nisabin Zakka ba to sai ayi sadaka kuma akwai lokutan Idi guda biyu na farko da idin babbar Sallah za a yi yanka a rabawa jama’a sadakar naman saboda haka muna yin addu’a ga Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yi kuma in mun yi Allah ya karba mana abin da muke karantar da jama’a Allah ya albarkace su.

Shaikh Zakariyya ya kuma yi addu’a ga manema labarai da suke yi wa jama’a aiki da Allah ya saka masu da alkairi ya Sanya albarka a cikin ayyukan da suke yi. Ya kuma yi addu’a ga yaya da cewa dukkan karatun addinin musulunci da mu ba mu yi na Allah yasa yayan mu su yi shi Allah ya Sanya mu gama da duniya lafiya ya Sanya Aljannah ta zama makomar mu kuma dukkan abin da ya ke shafar musulmi da ba dadin ji Allah ya yaye mana shi gaba daya.

Ina yi wa yan jarida da kuka zo kuka same ni babbar godiya kwarai, ina yi wa Allah godiya a bisa hakan.

Wannan karramawa da aka yi wa Shaikh Zakariyya Usman mutumin da ke da kamfanin “Kur’an on cassette” karramawar ta biyo bayan irin yadda kungiyar mawallafa jaridu da mujallu mai suna Arewa Publishers Fotum tun farko suka Karrama Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman da lambar karramawa sakamakon ayyukan alkairi domin ciyar da rayuwar al’umma gaba.

Hakika dai rayuwar Shaikh Zakariyya Usman abin koyi ce ga dukkan al’umma kasancewarsa mutum ne mai kokarin karantar da jama’a abin da Allah da mazonsa suka ce musamman ta hanyar tauhidi da kadaita ubangiji madaukakin Sarki.

“Ko mu manema labarai da muka je wajensa domin wannan bayar da karramawa a gare shi sai da muka amfana da dimbin ilimin addinin musulunci da kuma wadansu al’amuran yau da kullum da suke a cikin Najeriya har ma da wadansu kasashen waje.

About andiya

Check Also

Remain steadfast against security challenges” – CDS General Musa to army officers and men

  The Chief of Defence Staff , General Christopher Musa has tasked the Nigeria Army …

Leave a Reply

Your email address will not be published.