Home / Lafiya / An Karyata Jita Jitar Samun Mai Cutar Korona A Zariya

An Karyata Jita Jitar Samun Mai Cutar Korona A Zariya

Daga Imrana Abdullahi
Wata majiya mai karfi daga garin Zariya ta tabbatar mana cewa babu gaskiya acikin jita jitar da ake yadawa cewa an samu wani wanda ake zargi da kamuwa da cutar Korona a Zariya.
Ana ta yada jita jitar cewa wai da akwai wani mutum da aka samu daga wani kauye saboda haka ne wadansu mutane ke kira ga Gwamnati da ta hanzarta gudanar da cikakken bincike game da lamarin domin daukar matakin da ya dace.
Kamar yadda muka rika samun tambayoyi daga jama’a game da an samu mai cutar Korona a zariya.
Wakilinmu ya tuntubi wata majiyar da ya dace su san ko an samu wanda ya kamu da wannan Zargi da cutar, sai majiyar ta bayyana mana cewa hakika babu wani ABU mai kama da irin haka domin idan akwai dole sai sun san faruwarsa.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.