Home / Lafiya / Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ya Harbu Da Cutar Korona Bairus

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ya Harbu Da Cutar Korona Bairus

Daga Imrana Abdullahi Kaduna
Bayanan da ke fitowa daga gidan Gwamnatin Jihar Kaduna kuma daga bakin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I ya tabbatarwa duniya cewa ya harbu da cutar Covid 19 da ake kira Korona Bairus
Gwamnan Kaduna ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar da kansa mai dauke da sa hannunsa kuma gashi a cikin bidiyo yana tabbatarwa duniya cewa sakamakon kwajin da aka yi masa na Cutar Korona Bairus ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Korona bairus.
A cikin sanarwar Malam Nasiru ya bayyana cewa duk da ba zato ba tsammanin cewa yana dauke da cutar amma sai gashi ya harbu da cutar.
Gwamnan a cikin faifan bidiyon da ya bayyana ya sanar cewa mataimakiyarsa za ta ci gaba da aikin kwamitin da aka nada domin yaki da wannan Covid – 19 Korona Bairus.

About andiya

Check Also

An Yi Addi’oin Musamman  Domin Samun Zaman Lafiya A Katsina

 A ranar Litinin din  da ta gabata ne 1 ga watan Augusta shekara  ta 2022  …

Leave a Reply

Your email address will not be published.